Bola Tinubu: Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suke Tafi Rivers Yayin Da Wike Ya Tarbi Zababben Shugaban Kasa Tinubu

Bola Tinubu: Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suke Tafi Rivers Yayin Da Wike Ya Tarbi Zababben Shugaban Kasa Tinubu

Rivers - Hasashen da ake yi na cewar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi da kowa da kowa a cikin gwamnatin shi ya fara tabbata tun gabanin zuwan ranar 29 ga watan Mayu, wato lokacin da shugaba Buhari zai miƙa ma shi mulki.

Abinda ya faru a wannan ziyara ta kwana biyu da ya kaima gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya fara nuni da alamar cewa lallai sabon shugaban ƙasar zai zo da tsarin gudanar da gwamnatin haɗaka da zarar an rantsar da shi a 29 ga watan Mayu.

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu da Nyesome Wike wajen kaddamar da aiki a Rivers. Hoto: Tinubu/Shettima Media Support Group
Asali: Facebook

Baya ga cewa gwamnan PDP wato gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ne ya gayyace shi, haka nan ma akwai ƙarin wasu gwamnonin na PDP da suka halarcin taron a yayin ziyarar ta shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bola Tinubu Ya Baiwa Gwamna Wike Mamaki Kan Bukata 1 da Ya Nema

Gbajabiamila da gwamnoni biyar ne suka halarci taron

A tare da Tinubu kuma akwai kakakin majalisar dokoki wato Femi Gbajabiamila, da kuma gwamnoni biyar masu ci waɗanda suka haɗa da na PDP da kuma na jam’iyya mai mulki wato na APC. Legit ta tattaro sunayen gwamnonin da su ka samu damar halartar wannan taro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnonin da suka samu halartar taron sune:

Seyi Makinde

Gwamnan jihar Oyo kuma zaɓaɓɓen gwamna a zaɓen da ya gabata wato Seyi Makinde yana cikin gwamnonin da suka halarci taron. Makinde dai yana cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP musamman ma dai duba da cewa yana cikin waɗanda suka samu nasara a zaɓen da ya gabata.

Mohammed Badaru Abubakar

Gwamnan jihar Jigawa mai barin gado wato Badaru Abubakar na APC ma yana cikin wadanda su ka halarci wannan taro. Badaru dai ya yi tenuwa biyu ne a mulkin jihar Jigawa inda yanzu kuma haka ɗan takarar da ya tsayar a APC Umar Namadi ne yayi nasara a zaɓen da ya gabata.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana

David Umahi

Gwamnan jihar Ebonyi mai barin gado shima wani jigo ne a jam’iyyar APC. Baya ga samun nasarar da ya yi ta kujerar sanata da ya nema, Umahi ya yi kokarin kawo ma Tinubu kuri’u masu yawa gami da samun nasarar ɗan takarar gwamnan sun a APC a jihar duk kuwa da karfin jam’iyyar LP a yankin.

Hope Uzodinma

Gwamnan jihar Imo ma dai wani babban jigo ne na APC a yankin kudu maso gabas. Uzodinma dai wanda ya taɓa rike kujerar sanata a baya, kuma mai neman a ƙara zaɓen shi zagaye na biyu a zaɓen su da zai gudana a watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki.

Abdulrahman Abdulrazaq

Gwamna Abdulrazaq na jihar Kwara wanda shima ya sake ɗarewa kujerar shi a zagaye na biyu a zaɓen da ya gabata na cikin tawagar gwamnonin da suka mara ma Tinubu baya zuwa jihar ta Rivers.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Nyesom Wike

Uban taro dai shine gwamnan jihar ta Rivers wato Nyesom Wike duk da kasancewar shi dan jam’iyyar PDP. Wike dai shine ya jagorancin gwamnonin nan guda biyar da ake ma laƙabi da G5 waɗanda suka jajirce akan cewa dole sai mulki ya koma kudancin kasar nan daga Arewacin kasar.

“Bazan nuna wariya ga kowane yanki ba”: sabon alwashin da Tinubu ya sha ma kan shi

Da ya ke jawabi a wajen taron, Tinubu ya tabbatar ma da mutanen jihar Rivers cewa ba zai nuna wariya ga kowane yanki ba wajen ayyuka na cigaba.

Zaɓaɓɓen shugaban wanda ya kai ziyara ta kwana biyu jihar Rivers ya jinjina ma gwamna Wike bisa ayyukan raya kasa da yake yi.

Wata mata ta kashe kishiyar ta mai ɗauke da juna biyu

A wani labarin na daban kuma, jami'an tsaro a jihar Legas sun gurfanar da wata mata a gaban kotu bisa tuhumar ta da ake yi na kashe kishiyar ta mai ɗauke da juna biyu.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a unguwar Ilejo da ke yankin Ikorodun jihar ta Legas, inda wata mata saboda zafin kishi ta taka har gida sannan ta kashe amaryar mijin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel