Bola Tinubu Ya Ba Da Mamaki, Ya Yi Watsi da Bukatar Gwamna Wike

Bola Tinubu Ya Ba Da Mamaki, Ya Yi Watsi da Bukatar Gwamna Wike

  • Shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da bukatar da gwaamna Wike ya nema a wurinsa
  • Yayin ziyarar kwana biyu da ya fara yau, Wike ya roki gwamnatin Tinubu ta biya Ribas kuɗin ayyukan gwamnatin tarayyan da ta aiwatar
  • Sai dai Tinubu yace bai ɗauki alkawarin haka ba, amma gwamnan na iya bibiya don ya karba a gaba

Rivers - Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi abinda za'a iya kira da abun ban mamaki yayin maida martani ga bukatar gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

Ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, Tinubu ya ziyarci jihar Ribas domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka kuma ya samu tarba mai kyau daga Wike da manyan kusoshin gwamnati.

Tinubu da Wike.
Bola Tinubu Ya Ba Da Mamaki, Ya Yi Watsi da Bukatar Gwamna Wike Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya ƙi aminta da buƙatar Wike

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Bayan zuwan Tinubu, gwamna Wike ya miƙa kokon bara, ya roki gwamnatin shugaba mai jiran gado ta biya jihar Ribas kuɗin da ta kashe wurin gudanar da ayyukan FG a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake maida martabi kan bukatar Wike, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba zata ɗauki alkawarin tilasta wa kanta biyan kudin ayyukan da Ribas ta aiwatar wanda suke haƙƙin FG.

Zababben shugaban kasan ya faɗi haka ne a Patakwal, yayin kaddamar da gadar Rumuokuta, a wani bangaren ziyarar kwana 2 da ya fara a Ribas, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Tinubu ya shaida wa gwamna Wike cewa zai sake duba wannan buƙata da ya gabatar masa nan gaba amma ya ci gaba da bibiya yana tuna masa.

"Dangane da buƙatar da ka nema ta biyan kudin aiki, baku biyo ni bashin komai ba (ban ɗauki alkawarin biya ba)."

Kara karanta wannan

Toh fa: Tinubu ya watsar da 'yan APC, ya ce ba dan wani gwamnan PDP ba da ya fadi zabe

"Ba zaku girgiza ni na biya kuɗin ba, titinku ne, ku kuke rayuwa a waɗan nan Tituna. Na yaba da kokarinta, amma ka kama kafa da ni sai ka karɓa."

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari

A wani labarin kuma Tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana babban abinda ya yi nadama a mulkin Buhari

Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Buba Galadima, ya ce Buhari ya ƙara lalata fagen siyasa a Najeriya.

Ya ce a halin yanzun duk kirkinka da gogewarka ba zaka iya cin zaɓe ba matukar baka yi ruwan naira ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel