"Na Gaji": Wata Yar Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu, Sannan Ta Damƙa Mata Motocci Da Gidajen Mijinta

"Na Gaji": Wata Yar Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu, Sannan Ta Damƙa Mata Motocci Da Gidajen Mijinta

  • Wani magidanci da suka sa mu saɓani da matar shi ya sha alwashin maka ta kotu bisa zargin zambatarsa da ta ke shirin yi
  • Matar ta maka mijin na ta kotu inda ta bayyana cewa ita ba ta ra'ayin auren sannan ta buƙaci a mallaka ma ta kadarorin shi shekaru kaɗan da yin aurensu
  • Ta ɗauke gami da sauya sunan mijinta da sunan ta akan duka takardun kadarorin mijin ba tare da sanin shi ba

Wata mata ka iya fuskantar ƙalubale biyo bayan gano ta da mijin ta ya yi akan yunƙurinta na mallake duka kadarorin da ya mallaka sannan ta wancakalar da shi.

Wani mai amfani da Tuwita mai suna Oloye ne ya wallafa labarin a shafin shi na Tuwita wanda ya bayyana cewa mutumin ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Ingila bayan rabuwar shi da matar ta shi inda ya zo ya auri wata a nan gida.

Kara karanta wannan

"Na Wanke Shi Tas", Dirarriyar Budurwa Ta Yaudari Mahaifinta a Matsayin Budurwarsa, Ya Tura Mata Kudade

mata za ta kwace kadarar mijin ta
Wata Mata ta Nemi Kotu Ta Raba Auren Su, Sannan Ta Damƙa Ma Ta Kadarorin Mijin Hoto: Wirestock, Shua Taiwo, Don Mason, Westend61
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar da ya aura ta yi ƙarar shi a kotu ta na neman cinye dukiyar shi

Shekaru kaɗan da yin auren nasu sai matar ta yi ƙarar shi akan ya sake ta sannan kuma ta buƙaci a hannan ta ma ta kadarorin shi, ciki kuwa harda motoci na alfarma da kuma gidan shi wanda ta yi iƙirarin cewa duk na ta ne.

Oloye ya ce matar ta buɗe ma'ajiyar mijin ne inda ta ɗauki takardun na ainihi, kana ta je ta buga na bogi ɗauke da sunayen ta kamar yadda Legit ta wallafa.

Ta shaida ma kotu cewa ita ce fa ke da mallakin duk kadarorin tunda a yanzu haka ma ta riga da ta sanya sunan ta a kan shedar mallakin gidan da suke ciki.

Kara karanta wannan

Ba Alhakin Gwamnati Ba Ne Samar Da Aikin Yi Ga 'Yan Ƙasa, In Ji Kakakin Buhari, Femi Adesina

Lauyan mutumin ya cece shi da kwafin takardu na ainihi

Sai dai sa'a ɗaya da mutumin ya yi ita ce, lauyan shi ya na da kwafi na ainihin takardun, waɗanda da su ne kotu ta yi la'akari sannan kuma ta yi fatali da ƙarar da matar ta shigar.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakunan su a kan labarin, inda mafi yawa daga cikinsu su ka yaba da abin da mutumin ya yi. Daga ciki wasu sun buƙaci ya ɗauki hukunci a kan ta dangane da takardun na bogi da ta buga a kan kadarorin shi. Sai dai dama shi ma mutumin ya na shirye-shiryen maka matar a kotu bayan faruwar lamarin.

A kwanakin baya, Legit ta wallafa wani labari kan wani mutumi da ya bar matar shi da 'ya 'yan shi domin ya fara gudanar da sabuwar rayuwa.

A ranar 31 ga watan Disamban 2021 ne dai mutumin mai suna Alex ya bayyana cewa ya bar matar shi da su ka shafe shekaru takwas a tare ita da 'ya 'yan su guda biyu, gida mai ɗaki uku, mota, da komai-da-komai don sake sabuwar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel