Yan Ta'adda Sun Halaka Magajin Gari, Sun Sace Mutane da Dama a Jihar Kaduna

Yan Ta'adda Sun Halaka Magajin Gari, Sun Sace Mutane da Dama a Jihar Kaduna

  • Yan bindiga sun kashe Magajin Gari, sun yi awon gaba da dandazon mutane a Unguwan Liman, Birnin Gwari a Kaduna
  • Mazaunin garin ya ce maharan sun kai musu farmaki da misalin karfe 10:00 na daren ranar Lahadi
  • Har yanzun babu wani martani a hukumance daga gwamnati ko rundunar yan sandan jihar Kaduna

Kaduna - Wasu 'yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Unguwan Liman da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, shiyyar arewa maso yamma.

Yan bindigan waɗanda mahukunta a Najeriya suka ayyana a matsayin 'yan ta'adda sun kashe shugaban ƙauyen, watau Magajin Gari, kuma sun sace mutane da yawa.

Harin Kaduna.
Yan Ta'adda Sun Halaka Magajin Gari, Sun Sace Mutane da Dama a Jihar Kaduna Hoto: channels
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro a rahotonta cewa yan bindigan sun yi wa mazauna ƙauyen barazanar sake kawo musu hari nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Ashe Ba Daɗi: Sojojin Najeriya Sun Ɗanɗana Wa Yan Bindiga Ɗacin Mutuwa, Sun Kashe 15 a Jihar Arewa

Wani mazaunin ƙauyen Unguwan Liman, Malam Uban Marayu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin ya bayyana cewa maharan sun kutsa kai cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Lahadi kana suka aikata wannan ɗanyen aiki.

A cewarsa, 'yan ta'addan, waɗanda suka zo adadi mai yawa, sun yi awon gada da mazauna garin da dama.

"Sun shigo jiya (Lahadi) da daddare kusan ƙarfe 10:00 na dare, sun biyo ta gefen Birnin Gwari, suka kashe Magajin Garin Unguwan Liman, mai nisan kilomita 3 zuwa Birnin Gwari."
"Sun yi garkuwa da adadin da babu wanda ya san iyakarsu na mutanen garin (Maza da mata). A ƙauyen Kwanan Shehu da ke maƙota sun kwashi kaya a shaguna."

"Muna rokon rahama da kariyar Allah mai girma da ɗaukaka ta tabbata a kanmu," inji Malam Uban Marayu.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Wani Babban Jami'in Kotun Musulunci Ya Rasu Ta Hanya Mai Ban Tausayi a Watan Azumi

Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko rundunar 'yan sandan jihar kan wannan sabon harin da aka kai.

Vanguard ta ce har lokacin haɗa rahoton kakakin rundunar yan sandan Kaduna. Muhammad Jalige, bai ɗaga kiran waya ba kuma bai turo amsar sakonnin Tes ba.

Sojoji sun samu nasara a jihar Zamfara

A wani labarin kuma Yan Ta'adda 15 Sun Sheka Barzahu Yayin da Sojoji Suka Dakile Hari a Zamfara

Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da suka yi yunkurin kai hari kauyuka biyu a jihar Zamfara.

Dakarun soji da haɗin guiwar 'yan banga sun kai ɗauki cikin lokaci kuma suka sheƙe yan ta'adda akalla 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel