Tsirarun Mutane Sun Tashi da Naira Biliyan 20 a Kwamitocin Shugaban Kasa a Shekara 8

Tsirarun Mutane Sun Tashi da Naira Biliyan 20 a Kwamitocin Shugaban Kasa a Shekara 8

  • Gwamnatin tarayya tayi suna wajen kafa kwamitoci iri-iri da nufin shawo kan matsalolin Najeriya
  • Bincike ya nuna aikin wadannan kwamitoci ya ci wa kasar nan kudin da sun haura Naira biliyan 20
  • Mai kula da duk ayyukan da aka yi domin a iya kawo gyara shi ne sakataren gwamnatin tarayya

Abuja - Sama da Naira biliyan 20 aka warewa kwamitocin shugaban kasa da suka yi aiki a karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya na kasa.

Binciken da Punch ta gudanar ya nuna cewa an batar da biliyoyi a kan wadannan kwamitoci da suka yi aiki tsakanin shekarar 2015 da Afrilun 2023.

Masana sun yi Allah-wadai da yadda ake yawan kashe biliyoyi kudi domin daukar dawainiyar wadannan kwamitoci da ke karkashin kulawar ofishin SGF.

Shugaban bincike a cibiyar nazarin harkokin Sin, Charles Onunaiju ya ce ana kafa kwamitocin ne suyi aiki a dalilin gazawar hukumomin gwamnati.

Kara karanta wannan

Madallah: Wata kungiya ta rabawa talakawa 750 kayan abinci a wata jihar Arewa

Kwalliya ta na biyan kudin sabulu?

Onunaiju ya shaidawa jaridar cewa kwamitocin nan sun zama abin da suka zama, ana batar da kudi ba tare da an yi wani bayanin inda suka shiga ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zargin da ake yi shi ne ana kashe masu kudi masu yawa, ba tare da sun yi aikin a zo-a gani ba.

Shugaban Kasa
Shugaban Najeriya a taro Hoto: @MohdHAbdullahi
Asali: Twitter

Aliyu Ilias wanda masanin tattalin arziki ne kuma mai sharihi a kan al’ummar yau da kullum ya ce kwamitocin su na hana hukumomin gwamnati aikinsu.

Yayin da masana su ka tofa albarkacin bakinsu, ba a iya samun Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha domin jin ta-cewarsa a game da batun ba.

An yi kwamitoci 40

Rahoton ya ce a shekaru kusan takwas, Muhammadu Buhari ya kafa kwamitoci akalla 40 da suka yi aiki kan ilmi, kiwon lafiya, tattalin arziki da sauransu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta

Akwai kwamitin da ya yi aiki wajen rage talauci, akwai wanda ya yi gyara kan kiwon lafiya, akwai kwamitin da ya duba wadanda suka dace da lambar yabo.

Gwamnati ta kafa kwamitin gyara harkar kwallon kafa, akwai wanda suka yi aikin IPPIS baya ga kwamitin gyara TSA da wanda ya duba bukatun 'Yan ASUU.

'Yan majalisa za su ci N49bn

A wani rahoto da muka fitar a baya, an ji akwai ‘yan majalisar dokoki a jihohi 36 wanda adadinsu bai zarce mutum 700 ba, za su lamushe N16bn a shekaru hudu.

Sannan akwai ‘yan majalisar wakilan tarayya 360 da Sanatoci 109 da ake da su da za su tashi da N32bn. 'Yan majalisar Najeriya su na karbar alashi da alawus iri-iri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel