Gwamnatin El-Rufai Ta Dage Dokar Kulle Da Ta Sanya a Yankin Kaduna

Gwamnatin El-Rufai Ta Dage Dokar Kulle Da Ta Sanya a Yankin Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar zaman gidan da ta sanya a wani yankin ƙaramar hukumar Chikun
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce jami'an tsaro za su ci gaba da sintiri a yankin don tabbatar da tsaro
  • A ranar Litinin gwamnatin Kaduna ta sa dokar ta tsawon awanni 12 a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya sakamakon kashe rai 2

Kaduna - Gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin gwamna Malam Nasiru El-Rufai ta ɗage dokar kulle da ta sanya a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya da ke karamar hukumar Chukun.

Leadership ta tattaro cewa tun da fari gwamnatin ta ƙaƙaba dokar zaman gida tsawon awanni 12 a yankin biyo bayan rikicin da ya barke har aka rasa rayukan mutum 2.

Malam Nasiru.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai Hoto: Governor Kaduna
Asali: UGC

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ne ya tabbatar da cire dokar a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar 8 ga watan Afrilu, 2023.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Wani Fursuna da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje Yana Aikata Sabon Laifi

Ya ce gwamnati ta cire dokar kulle tsawon awanni 12 a Sabon Garin Nasarawa- Tialrkaniya daga yau Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mista Aruwan ya kara da cewa Sojoji da 'yan sanda zasu ci gaba da Sintiri a yankunan Anguwar yayin da mutane ke da yancin ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Channels tv ta rahoto kwamishinan na cewa:

"An cire dokar kullen awanni 12 da aka sanya a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya, ƙaramar hukumar Chikun daga ranar Asabar 8 ga watan Afrilu, 2023."
"Jami'an rundunar soji da 'yan sanda zasu ci gaba da sintiri a yankunan Anguwar, yayin da mazauna yankin suka samu yancin ci gaba da harkokinsu na yau da kullum."
"Gwamnati na shawartan mutane su guji duk wani abu da zai kai ga ta da zaune tsaye, domin duk wani abu makamancin haka zata ɗauki mataki a kai bisa tanadin doka."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

A ranar Litinin da ta shige, gwamnatin Kaduna ta ƙaƙaba dokar kulle a yankin karamar hukumar sakamakon rikicin da ya kai ga kisan kai.

Wani mazaunin Tirkaniya ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa sun ji daɗi da aka cire dokar domin zasu ci gaba da harkokinsu kamar baya amma yace yana tsoron tashin rikicin.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya bayanansa ya ce ɗaya daga cikin mutum 2 da aka kashe a layinsu ya ke, ɗayan kuma a gaban layinsu.

Ya ce:

"Mun ji daɗin wannan mataki, da farko an hana mu fita awanni 24, mun sha wahala, aka rage zuwa awanni 12, yanzu kuma an cire baki ɗaya, muna fatan zaman lafiya ya dawo."
"Har yanzun sojoji na yawo a yankunan Anguwar mu amma ba ruwansu da kowa, rikicin babu daɗinji ko kadan, ɗaya daga cikin waɗanda aka ƙashe ba ruwansa, kawai ya tsoma baki ne domin a yi sulhu."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Kasurgumin fursunan da ya tsere a magarkamar Kuje ya sake shiga hannu

An kai hari sansanin 'yan gudun hijira

A wani labarin kuma Yan Bindiga Makiyaya Sun Kai Sabon Mummunan Hari Kan Yan Gudun Hijira a Benue

Wasu mahara ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutane sama da 40 a sansanin 'yan gudun Hijira da ke ƙaramar hukumar Guma a jihar Benuwai.

Lamarin ya faru da daren ranar Jumu'a kuma har yanzun gwamnatun jihar ko hukumar yan sanda ba su ce komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel