An Ga Jinjirin Watan Ramadana a Wasu Yankuna Daban-Daban Na Najeriya, Inji Kwamitin Ganin Wata

An Ga Jinjirin Watan Ramadana a Wasu Yankuna Daban-Daban Na Najeriya, Inji Kwamitin Ganin Wata

  • Kwamitin duban wata a Najeriya ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadana na wannan shekarar da ake ciki
  • Sarkin Musulmi ya bayyana gobe Alhamis 23 ga watan Maris a matsayin ranar farko ta watan Ramadanan hijira 1444
  • A baya, sarkin ya shawarci Musulmai da su fara duban watan tun daga ranar 22 ga watan Maris na wannan shekarar

Jihar Sokoto - Kwamitin duban wata a Najeriya (NMSC) ya bayyana cewa, an ga jinjirin watan Ramadana a wasu yankuna daban-daban na Najeriya.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata gajeriyar sanarwar da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Facebook a ramar Laraba 22 ga watan Maris da dare.

An ga watan Ramadana a Najeriya
An ga wata a Najeriya gobe za a fara azumi | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

“Kwanitin duban wata yana sanar da rahoton cewa ya zuwa yanzu an samu rahoton ganin jinjirin watan Ramadana na 1444H daga yankuna daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ba a Ga Jinjirin Wata Ba a Kasar Saudiyya, Azumin Ramadan Zai Fara Ranar Alhamis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Alhamdu Lillah. Taqabbalallahu Minna Wa Minkum. Allah ya datar damu da albarkar watan gaba dayanmu ya kuma ba mu damar girbar tagomashin da ke cikinsa. Amin.”

Hakazalika, kwamitin ya ce, nan ba da jimawa Sarkin Musulmi zai sanar da ganin watan a hukumance.

Sarkin Musulmi ya yi sanarwar ganin wata

A bidiyon da muka samo daga jaridar Daily Trust, an ji lokacin da Sarkin Musulmi na Najeriya yake sanar da ganin watan a Najeriya.

Hakazalika, sarkin ya taya Musulman Najeriya zagayowar watan Ramadana, tare da fatan Allah ya dawwamar da zaman lafiya ga kasar.

Kalli bidiyon:

Wannan sanarwar na nufin, gobe Alhamis 23 ga watan Maris ce 1 ga wtan Ramadana a hijira 1444 ta Annabi SAW.

Musulman duniya na azumuntar kwanaki 29 ko 30 na watan Ramadana a duk shekara, watan da kekara kusantar da Musulmi da ubangijinsa.

Kara karanta wannan

Azumin bana: Sarkin Musulmi ya fadi ranar da ya kamata a fara duban jinjirin wata

A fara duban wata, inji sarkn Musulmi

A wani labarin, kun ji tun farko yadda sarkin Musulmi ya ba da umarnin a fara duban watan Ramadana daga ranar 22 ga watan Maris, 29 ga watan Sha’aban kenan.

Ya bayyana bukatar ‘yan kasar su ci gaba da yi mata addu’ar alheri da kwanciyar hankali game da zaman lafiya dawwamamme a wannan yanayin.

Najeriya na fuskantar matsalar tsaro, tattalin arziki da dai sauran abubuwan da ke ci gaba da tada hankalin ‘yan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel