Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

  • Sabon rikici ya barke tsakanin wasu kabilai a kananan hukumomin Ussa da Takum na jihar Taraba
  • A rikicin na baya-bayan nan, mutane a kalla 17 sun riga mu gidan gaskiya kamar yadda wasu yan garin suka tabbatar
  • A yan kwanakin nan wasu matasa sun kona fadar wani basarake a Taraba da suke zargi yana hada baki da mahara

Taraba - Wasu da aka zargin mayakan sa-kai ne sun salwantar da rayyukan mutum 17 a harr-hare daban da garuruwan da ke kananan hukumomin Takum da Ussa a jihar Taraba, rahoton The Punch.

Harin wanda ya faru tsakanin ranar Lahadi da jiya Talata ya janyo kona fadar basarake da kona motoccin mai sarautan gargagiya da fusatattun matasa suka yi.

CP Kwamishinan
Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Dan Basaraken Kano

The Nation ta rahoto hare-haren na baya sun sake barkewa tsakanin kabilu biyu a yankin wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi tsohon rikici ne.

Mazaunin Taraba ya magantu kan yadda abin ya faru

Wani mazaunin garin, KM Kasman, wanda ya yi magana da The Nation, ya ce hare-haren sun faru ne bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi tsakanin bangarorin biyu.

Ya ce an sheke mutum shida a daren ranar Lahadi yayin da a daren ranar Lahadi an halaka wasu takwas ciki har da mai maganin gargajiya da ke dawowa gida daga wan taro.

Kasman ya ce:

"An kashe mutum shida amma dattawa sun yi roko kada wanda ya dauki fansa. A daren ranar Lahadi, a wurin da na farkon ya faru, an kashe mutum takwas. Bakwai cikinsu da aka kashe a hanyar Kwesati masu maganin gargajiya ne da suka tafi taro suke dawowa gida. Bayan hakan, a wani garin manoma, Fikyu, an tsinci gawa uku da raunin adda a jikinsu.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

"Matasa sun tafi wurin basaraken garin sunyi korafi da cewa za su dauki fansa. Sun nemi sanin dalilin da yasa ya ke hana su daukan fansa da abin da ya sani kan hare-haren. An samu rashin jituwa har ta kai ga kona fadarsa.
"Matasan na ganin akwai hadin baki tsakanin basaraken (Kwe Ado na Masarautar Lisam) da maharan.
"Eh, misalin karfe 6.30 na yamma, maharan sun yi kokarin kai hari Achanyim a Takum amma matasa sun dakile harin. Yanzu dai komai ya lafa amma za a sake bitan yarjejeniyan zaman lafiya tsakaninsu yau."

A cewarsa, hanyar Tati a karamar hukumar Takum ta zama abin tsoro cikin makonni biyu da suka wuce saboda mahara na tare mutane.

Martanin yan sanda

An yi kokarin ji ta bakin ciyaman din karamar hukumar Ussa don ji ta bakinsa amma abin ya ci tura.

Shima mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba ba a samu ji ta bakinsa ba dangane da lamarin. Bai amsa sakon kar ta kwana da aka tura masa ba yayin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Ya ce:

"Amma mataimakin karamar hukumar Takum, Emmanuel Matuidi. Abin ya faru amma dai a Ussa ne, bai kai karamar hukumar Takum ba."

Yan bindiga sun halaka mutum 10 a wani hari a Taraba

A baya kun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga sun halaka mutane 12 a wani harin da suka kai karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru a karamar hukumar Mubizen a wata rugar makiyaya fulani a masarautar Pangri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel