Kudin Tsaro: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, ICPC, FIRS, CBN a Ranar Talata

Kudin Tsaro: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, ICPC, FIRS, CBN a Ranar Talata

  • A yanzu haka gwamnonin Najeriya na shirin ganawa da CBN, EFCC da sauran hukumomin tsaro
  • Rahotanni sun ce gwamnonin za su gana da hukumomin tsaro domin tattauna batutuwan da suka danganci kudin tsaro da aka turawa jihohi
  • Kudin tsaro wani kaso ne da ake turawa gwamnatocin jiha duk wata don inganta tsaro a jihohinsu

Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya karkashin inuwar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suna shirin ganawa da jami'an babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da sauransu don magance batutuwan da suka shafi kudin tsaro.

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta hannun shugabanta kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ce ta sanar da hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Afrilu, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamnonin Najeriya a cikin taro
Kudin Tsaro: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, ICPC, FIRS, CBN a Ranar Talata Hoto: Nigeria Governors Forum
Asali: Facebook

Dalilin ganawar

Tambuwal ya bayyana cewa ganawar wacce aka shirya yi a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, kamar yadda katin gayyatar da darakta janar na kungiyar, Asishana Okauru, ya aika zai gudana ne ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

IPAC Ta Yi Martani Yayin da DSS Ta Gano Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce za a yi taron ta yanar gizo ne don tabbatar da ganin cewa dukkanin jami'an da abun ya shafa sun samu damar hallara, Channels TV ta rahoto.

A cikin wata sanarwa, kakakin NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya ce:

"Wadanda aka gayyata zuwa taron sun hada da EFCC, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da sauran hukumomi masu alaka, hukumar tattara kudaden shiga ta kasa, da CBN."

Yan bindiga sun farmaki garuruwan Neja, sun kashe mutum 7 da sace wasu da dama

A wani labarin kuma, wasu tsagerun yan bindiga sun kai farmaki garuruwa bakwai a karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja inda suka tafka ta'adi.

Maharan dai sun halaka akalla mutane bakwai sannan suka yi awon gaba da wasu da yawansu ya kai 26 lamarin da ya tilastawa mazauna yankunan da dama barin gidajensu.

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

Da yake tabbatar da faruwar mummunan al'amarin, Ciyaman na karamar hukumar Mashegun, Hon Umar Jibrin Igede, ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Maris an kashe tare da sace daruruwan mazauna yankin.

Yanzu haka wadanda suka gudu suka bar gidajensu sun koma samu mafaka a sansanin yan gudun hijira da ke Kontagora da sauran yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel