Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Basarake Saboda ‘Sukar Gwamnan APC a WhatsApp’

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Basarake Saboda ‘Sukar Gwamnan APC a WhatsApp’

  • Mai martaba Ekene Obinali ya fada hannun ‘yan sanda a dalilin aika wani sako a zauren WhatsApp
  • Ana zargin Basaraken na Umucheke a karamar hukumar Ideato ta Kudu da cin mutuncin Gwamna
  • ‘Yan Sanda su na tuhumar Obinali da cewa sakon da ya yada, yana sukar Gwamna Hope Uzodinma

Imo - Dakarun ‘yan sandan Najeriya sun kama Basarake a Kudu maso gabashin Najeriya saboda zargin yada mugun sako a dandalin WhatsApp.

Premium Times ta ce jami’an ‘yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane ne suka yi ram da Basaraken kasar Umucheke a garin Ideato a jihar Imo.

Ana zargin Mai martaba Ekene Obinali ya aika wani sako a dandalin sada zumunta na zamanin, inda aka soki Gwamnan Imo watau Hope Uzodinma.

Rahoton ya ce a ranar 20 ga watan Maris ne Basaraken ya taimaka wajen aika wannan sako a wani zaure na ‘Ideato Voice’ a dandalin WhatsApp.

Kara karanta wannan

To fah: Daga sukar gwamnan APC a WhatsApp, basarake ya kare a hannun 'yan sanda

An cafke Sarki, Vitus Ezenwa

Majiya ta ce ganin abin da sakon ya kunsa, hakan ya jawo Sarkin Umucheke ya fada hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai lura da wannan zaure na WhatsApp, Vitus Ezenwa ya tabbatarwa manema labarai cewa wannan lamari ya jefa Basaraken a cikin matsala.

Gwamna
Gwamna Hope Uzodinma a Aso Rock Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Mista Ezenwa wanda mawallafin jarida ne ya ce a ranar Laraba, 29 ga watan Maris 2023, aka cafke Mai martaba, jami’an ‘yan sanda suka tsare shi.

Sun ta ce Ezenwa ya na cikin wadanda aka tsare, amma daga baya aka bada belinsa da sharadin cewa zai rika kai kan shi gaban ‘yan sanda a kullum.

Me yayi zafi haka?

Mai magana da yawun dakarun ‘yan sandan Imo, ACP Henry Okoye ya shaida cewa ana binciken Mai martaba da zargin bata suna ta yanar gizo.

Sahara Reporters ta ce abi da sakon ya kunsa shi ne zargi a kan rawar da jagora a APC, Ahmed Gulak ya taka wajen zaman Uzodinma Gwamna.

Kara karanta wannan

Jifan 'yan sanda: An kama daliban Zakzaky da yawa a wurin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba

Sakon mai suna “Gov Hope Uzodinma in fresh scandal” watau Gwamna Uzodinma ya fada ragar sabuwar badakala ya jefi Marigayi Gulak da zargi.

Marigayin ne ya shiya zaben tsaida gwani na ‘dan takarar Gwamnan Imo a 2018 da Sanata Uzodinma ya yi nasara, a karshe aka bindige shi a 2021.

EFCC v Tsohon VC a Najeriya

Rahoto ya tabbatar da cewa hukumar EFCC ta kai Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Shehu Usman kotu da zargin satar wasu N998, 000,000.00.

Ana zargin tsohon shugaban jami’ar ABU da jami’in kula kudi da hannu wajen cin amana da satar kudi, su ma kotu ta bada belinsu da sharadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel