'Yan Sanda Sun Kama Daliban Zakzaky 19 a Kan Yin Zanga-Zanga Birnin Tarayya Abuja

'Yan Sanda Sun Kama Daliban Zakzaky 19 a Kan Yin Zanga-Zanga Birnin Tarayya Abuja

  • ‘Yan sanda sun kame daliban Zakzaky 19 a babban birnin tarayya Abuja a lokacin da suke zanga-zanga
  • Wannan ya zo ne bayan da aka yi hukunci kan batun fasfo din malamin ‘yan Shi’a a Najeriya da ya jima yana tsare
  • Ya zuwa yanzu, ‘yan sandan sun ce za su gurfanar da daliban na Zakzaky domin hukuntasu yadda ya dace

FCT, Abuja - Yayin da ‘yan Shi’a suka barke da zanga-zanga a Abuja ranar Alhamis, ‘yan sanda sun ce sun kame daliban Zakzaky 19 bisa zargin tada hankalin jama’a da barna a birnin.

Hakazalika, rundunar ta ce za a gurfanar da daliban nasa a kotu bisa zargin yin zanga-zanga ba bisa ka’ida da neman izini ba kamar yadda doka ta tanada da kuma lalata kayan gwamnati.

Wannan batu dai na fitowa ne daga bakin mai magana da yawun ‘yan sanda, SP Josephine Adeh a cikin wata sanarwa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Yan Obidients Sun Shirya Zanga-Zangar Zaben 2023 a Fadar Shugaban kasar Amurka

'Yan shi'a sun shiga hannu a Abuja
Shugaban 'yan Shi'a Zakzaky da matarsa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadda batun ya fara

A cewar ‘yan sanda, ‘yan Shi’an sun fito zanga-zanga ne bayan hukuncin babban kotun tarayya game da fasfo din malaminsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ruwaito cewa, daliban nasa sun zo su sama da 400, inda suka mamaye hanyoyi da ke kai wa ga kotun da kuma Eagle Square suna zanga-zanga.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, abin da suka yi ya jawo mummunan cunkoso da kuntatawa masu wucewa a birnin.

Abin da daliban Zakzaky ke nema

Sanarwar ta bayyana cewa, daliban na Zakzaky suna yin zanga-zangar ne don tabbatar da an saki fasfo din malamin nasu da a baya ya shafe shekaru yana tsare, Daily Post ta ruwaito.

A lokacin da suke tsaka da zanga-zangar ne ‘yan sanda suka samu labari, inda suka yi gaggawar zuwa wurin tare da kame wasu daga cikinsu; mutum 19.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Hakazalika, rundunar ta ce, daliban na Zakzaky sun yi jifa kan jami’an tsaro da kadarorin gwamnati, wanda hakan ya saba doka.

Za a tabbatar da tsaro a Abuja

Daga karshe dai rundunar ta ce, ta shirya tsaf domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a birnin, inda ta ta ba da lambobin waya kamar haka; 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883 don tura koke da korafi.

Wani rahoto da muka wallafa a baya ya bayyana yadda aka kashe ‘yan Shi’a jama’ar Zakzaky a jihar Kaduna bayan da suka yi arangama da tawagar gwamna El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel