EFCC ta Maka Tsohon Shugaban Jami’ar ABU Zariya a Kotu Kan ‘Satar’ Naira Biliyan 1

EFCC ta Maka Tsohon Shugaban Jami’ar ABU Zariya a Kotu Kan ‘Satar’ Naira Biliyan 1

  • Hukumar EFCC ta shiga kotu da Farfesa Ibrahim Garba wanda ya taba rike Jami’ar ABU Zariya
  • Ana tuhumar Ibrahim Garba da Ibrahim Shehu Usman da hannu wajen yin gaba da kusan N1bn
  • EFCC mai yaki da marasa gaskiya ta ce tsakanin 2013 zuwa 2016, an sace kudin gyaran wani otel

Kaduna - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta gurfanar da tsofaffin shugabannin jami’ar ABU Zariya a kotu.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar a shafukanta a ranar Laraba, an ji cewa an yi karar Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Shehu Usman a kotu a garin Kaduna.

Hukumar ta na tuhumar tsohon shugaban na ABU Zariya da babban jami’in kula da kudi da hannu a badakalar satar Naira biliyan daya da suka tafka a ofis.

Mai magana da yawun bakin Wilson Uwujaren ya ce an jefi wadannan mutane biyu da zargi tara da suka shafi hannu wajen karkatar da dukiyoyin jami’ar.

Ana zargin an ci kudin gyaran otel

A cewar Wilson Uwujaren, mutanen da ake zargi sun yi sama da fadi da kudin da aka ware da nufin gyaran otel din jami’ar, Kongo Conference Hotel a Zariya.

Premium Times ta ce ana zargin hakan ya faru ne tsakanin shekarar 2013 da 2016. Legit.ng Hausa ta fahimci Farfesa Ibrahim Garba ya shiga ofis ne a 2015.

EFCC.
Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Shehu Usman a hannun EFCC Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Da aka je gaban Alkali, Farfesa Garba da Ibrahim Usman sun nuna ba su aikata laifuffukan da ake kararsu a kai ba, R.M Aikawa yake sauraron shari’ar.

Alkali ya bada belinsu a kotu

Mai shari’a M Aikawa ya bada belinsu a ranar Laraba, ya daga sauraron shari’ar a babban kotun tarayya da yake Kaduna sai zuwa 20 ga watan Yunin 2023.

Rahoton The Cable ya ce nan da kusan watanni uku za a koma kotu domin cigaba da shari’ar, inda ake tuhumar wadannan mutane biyu da satar N998, 000,000.

EFCC ta ce su na da hannu wajen cin amana, sabawa dokar yawo da kudi ta kasa. Alkali ya karbe masu fasfo, kuma za su rika zuwa ofishin EFCC duk Litinin.

Lauyan gwamnati ya ce tsofaffin shugabannin jami’ar syn boye N119,923,730.00 a cikin asusun wani kamfani na USIG NIGERIA LIMITED a bankin FCMB.

Pantami ya ce ana cikin barazana

Bankin Duniya ya ce nan da shekarar 2025, darajar tattalin arzikin zamanin Afrika zai kai $180b. Isa Ali Ibrahim Pantami aka rahoto ya na wannan bayani.

Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya ce barnar da miyagu suka yi a Intanet a shekarar nan ya karu da 300%, hakan ya jawo Ministan sadarwar Najeriyan ya koka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel