An Dena Ba Wa Mutanen Mu Gidan Haya Anambra, In Ji Miyetti Allah

An Dena Ba Wa Mutanen Mu Gidan Haya Anambra, In Ji Miyetti Allah

  • Shugaban kungiyar MACBAN shiyyar kudu maso gabas ya ce an daina ba wa yan kungiyar hayar gidaje a Jihar Anambra
  • Da yake jawabi a wajen taya Gwamna Soludu murnar cika shekara daya da kama aiki, jagoran Miyetti Allah ya ce akwai yankuna da dama da su ke hana yan kungiyarsu hayar
  • Kungiyar ta kuma yi kira da gwamnan ya shiga lamarin gudun kada abin ya zama wani abu na daban da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar al'umma a jihar

Jihar Anambra - Yan kungiyar makiyayi ta Najeriya Miyetti Allah (MACBAN) a Anambra ta ce ba a ba su hayar gidaje, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban Miyetti Allah a Kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Siddiki, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai lokacin da ya halacci bikin cikar Gwamna Charles Soludo shekara daya a ofis.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Taya Tinubu Murna Bayan Kwana 21, Ya Nemi Bukata 1 a Gwamnatinsa

Kungiyar MACBAN
An Dena Ba Wa Mutanen Mu Masauki A Anambra, In Ji Miyetti Allah. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bikin wanda ya gudana a Awka, babban birnin jihar, ya samu halartar manyan baki.

Siddikk ya bayyana Anaku, Umueje, Omor, Igbakwu, Omasi, Umumbo, Umuerum da Ifite-Ogwari duk a karamar hukumar Ayamelum a matsayin yankunan da aka hana mamboninta na Meyetti Allah matsuguni.

Ya yi kira ga gwamnan da ya shiga lamarin saboda a zauna lafiya a matsayin daya.

Siddiki ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin yan kungiyar da yan asalin garin duk da ''wasu abubuwan sabanin fahimta.

''Mu na son yankin ne saboda tattalin arziki ya habbaka. Babu wani makiyayi da ke da sha'awar shiga rigimar fili da yan asalin gari a fadin jihar.
Mu na kira jami'an yan sanda da DSS da su kai dauki duk lokacin da su ka ji labarin barkewar rikici tsakanin yan kungiyarmu da mutanen gari a fadin jihar.''

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

Shugaban Miyetti Allah, ya ce, har yanzu akwai bukatar a sanya ido don tabbatar da yan kasa ma su bin doka, har da makiyaya, sun gudanar da harkokinsu ba tare da iyaka ba a jihar.

A cewarsa, a matsayin su na makiyaya su na bukatar muhalli mai tsaro don yin kiwon su.

''A shirye mu ke mu taimaka yan asalin gari iya yadda su ke bukata, don samar da rayuwa mai ma'ana ga kowa da kuma dorewar zaman lafiya a jihar.'' in ji Siddiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel