Hukumar EFCC Ta Kama Masu Sayar POS 80 da Ke Siyar da Takardun Naira a Jihar Ondo

Hukumar EFCC Ta Kama Masu Sayar POS 80 da Ke Siyar da Takardun Naira a Jihar Ondo

  • An samu tsaiko a jihar Ondo, yayin da jami’an EFCC suka kwamushe masu sana’ar POS da yawa
  • Wannan ya faru ne sakamakon gano yadda wasu ke saye da siyar da takardun Naira a kasar nan
  • An yi sauyin kudi a Najeriya, ana ci gaba da fuskantar kalubalen karancin sabbin kudade da sabbi

Najeriya - Akalla mutum 80 aka kama masu sana’ar hada-hadar kudi ta POS bisa zargin suna saye da siyar da takardun Naira kan farashi mai tsada.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ne ta kama wadannan ‘yan Najeriya a jihar Ondo da ke Kudu masu Yamma.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, jami’an EFCC sun yi wannan aikin kamen ne a birnin Akure da ke jihar a karshen makon nan.

Yadda aka kama masu siyar da kudi a Ondo
Kudaden da aka buga a Najeriya sun zama magani | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Jami’an na EFCC sun karade yankin Akure ta Kudu da ta Yamma a jihar, inda suka kama masu siyar da kudin kan farashi mai tsada mara misaltuwa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye ya faru bayan wannan kamen?

Bayan wannan kamen, da yawan masu sana’ar POS a yankin sun ki bude shagunansu bisa tsoron zuwa a kwamushe su.

Na tsawon makwanni kenan a Najeriya, masu sana’ar POS na yawan sayen kudade daga bankuna tare da siyarwa jama’a a kasuwanni a farashi mai tsada.

Wannan kuwa ya faru ne sakamakon karancin takardun Naira da ya karade kusan ko’ina a kasar.

Wani ganau da ya ga kamen EFCC ya ce, jami’an sun yiwa kasuwar Oja-Oba da ke kusa da hanyar Oba Adesida a Akure kawanya ne tare da kama mutanen.

Yadda aka gano masu saye da siyar da kudi

Wani ganau na daban ya shaida cewa, wata mata ce ta zo ta tsaya tare da tambayar mai POS din nawa ne farashin cire N1000.

Ya kara da cewa:

“A lokacin da suka gama harkallar, sai matar ta yiwa wasu maza alama sannan ne na san ashe jami’an hukumar EFCC ne kuma daga nan suka tafi da mai shagon.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan ta'adda sun kone wani babban kotu a wata jiha, sun barnata kayan aiki

A halin da ake ciki, masu sana’ar POS na ci gaba da cin kakarsu, domin kuwa suna iya karbar ribar N300 kan takardun Naira ta 1000.

Yadda bankuna suka fara aiki a ranakun karshen mako

A bangare guda, binciken da Legit.ng Hausa ta yi ya nuna cewa, bankuna a jihar Gombe sun bude tare da ba mutane takardun kudi.

A bankin Access da ke bakin babbar kasuwa, wakilinmu ya ga yadda ake layin shiga bankin, kuma tabbas ana ba da kudin cikin tsanaki.

Sai dai, bankin ya rufe ne da misalin karfe 2 ba rana, wanda hakan ya bar kwastomomi da yawa a bakin bankin suna tsaye.

Khadija Usman, wata da ta je cire kudi a bankin na Access ta ce:

"Na samu shiga, an ba ni N20,000. Mun ji dadi da aka ce mu zo a karshen mako, kuma babu layi da yawa kamar na ranakun sati."

Kara karanta wannan

Ku rantse za ku zabe mu: Yadda 'yan siyasa ke yarjejeniya da jama'a kafin siyan kuri'unsu da taliya a Neja

Asali: Legit.ng

Online view pixel