Za Mu Hukunta Duk Musulmin Kano Da Muka Kama Yana Cin Abinci A Bayyane Yayin Ramadan, In Ji Hisbah

Za Mu Hukunta Duk Musulmin Kano Da Muka Kama Yana Cin Abinci A Bayyane Yayin Ramadan, In Ji Hisbah

  • Hukumar Hisba ta gargadi ma su cin abinci da rana a lokacin Ramadan za su sa kafar wando daya da ita
  • Hukumar ta kuma watsa jami'an ta zuwa masallatai lokacin azumin don kiyaye lafiyar al'umma a lokitan ibadah
  • Hukumar ta kuma bukaci al'umma su cigaba da tallafawa mabukata da abubuwan da Allah ya sawwake musu don rage musu radadi

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce za ta saka kafar wando daya da duk wanda ta kama ya na cin abinci lokacin azumi watan ramadan a jihar, rahoton The Punch.

Hukumar ta rarraba jami'anta zuwa masallatai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi lokacin watan Ramadan.

Jami'an Hisbah
Ba za mu raga wa duk musulmi da muka kama yana cin abinci a bainar jama'a ba yayin Ramadan, Hisbah ta Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kakakin hulda da jama'a na hukumar, Alhaji Ibrahim Lawan, ya fitar ranar Alhamis a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam El-Rufai Ta Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Siyasa Dake Shirin Ta Da Yamutsi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban kwamandan hukumar, Dakta Harun Ibn-Sina, ya ce:

''Jami'an Hisbah za su ziyarci masallatai lokacin buda baki, Tarawih, da kuma Tahajjud don kiyaye ma su bauta daga bata gari.
''Ma su tada hankulan al'umma lokacin wata mai tsarki za su dandana kudar su. Wasu daga cikin matasa ma su cin abinci a bainar jama'a lokacin azumi su ma baza mu raga mu su ba.''

Shugaban Hisbah na Kano, Ibn Sina ya yi kira ga al'ummar musulmi su taimakawa marayu da mabukata

Ibn-Sina ya yi kira ga dukkan al'umma da su taimaki marayu da mabukata, don rage mu su radadi.

Ya ce ciyarwa a cikin watan mai alfarma akwai lada daga wajen Allah(SWT), saboda ya na bude kofofin aljanna. Saboda haka akwai bukatar a dinga ninka ayyukan alheri saboda Allah.

Ibn-Sina ya ce tufatarwa, kayan abinci, hatsi, ruwa, da kudi su ma za a iya rabawa mabukata, kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Umurci Masu Tattaki Zuwa Kano Taya Shi Murna Su Dakata, Ya Fadi Abu 1 Da Ya Ke Son Su Mishi

Jami'an Hisbah sun shiga daki-daki don neman masu aikata ayyukan badala a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar ta Hisbah a Kano sun yi wan bincike na kwa-kwaf inda suka rika shiga daki-daki a Hills anda Valley, wani wajen shakatawa da bude ido a Dawakin Kudu da ke Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel