Hukumar EFCC Ta Cafke 'Yan Yahoo-Yahoo Da Dama a Jihar Kwara

Hukumar EFCC Ta Cafke 'Yan Yahoo-Yahoo Da Dama a Jihar Kwara

  • Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun samu nasarar cafke wasu ƴan Yahoo-Yahoo a jihar Kwara
  • Jami'an hukumar sun samu wannan nasarar ne a wani sumame da suka kai a maɓoyar ɓata garin
  • Daga cikin ɓata garin masu wannan ɓaƙar sana'ar da aka samu nasarar yin ram da su har da wani malamin addini

Jihar Kwara- Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun yi babban kamu a birni Ilorin na jihar Kwara.

Jami'an na EFCC a ranar Alhamis sun samu nasarar cafke wasu mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan damfarar yanar gizo wato Yahoo-Yahoo. Rahoton Leadership

Yahoo
Hukumar EFCC Ta Cafke 'Yan Yahoo-Yahoo Da Dama a Jihar Kwara Hoto: Leadership
Asali: UGC

Cafke ɓata garin wanda aka samu nasarar gudanar da shi a unguwar Mandate, cikin birnin Ilorin, ya biyo bayan samun bayanan sirri da akayi kan ayyukan da ƴan damfarar suke aikatawa a unguwar.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

Binciken farko da aka gudanar ya bayyana cewa daga cikin ɓata garin da aka cafke akwai wani malami, tagwaye, ɗalibai shida na makarantar gaba da sakandire daban-daban, mai haƙar ma'adanai da dai sauran su. Rahoton Punch

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sunayen waɗanda ake zargin sune Toheeb Albarka (malami); Lambe Kehinde da Lambe Taye; Francis Stephen; Olabode Yusuf, da Musbaudeen Akorede.

Masu yin karatu a makarantun gaba da sakandire daga cikin su sune: Moshood Okunola; Kayode Aderemi; Ayobami Olorunfemi; Paul Ayomide; Agboola Marvellous, da Adebisi Olatunde.

Sauran sun haɗa da Olaleye Solomon (mai haƙar ma'adanai); Akinade Samuel; Damilola Shagaya; Muhammed Awal; Adam Mubaraq; Ogundiran Nathaniel; Jamiu Ishola; Dauda Tunde; Abdullahi Sikiru; Kasali Adegoke; Jordan Adeyinka, da kuma direba, Ojeniyi Boluwatife.

Ragowar ƴan waɗanda ake zargi da damfanar sune, Adedamola Samson; Olarewaju Taofeek; Adewale Oloro, da Omogbolahan Ibrahim.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun su sun haɗa motoci tsala-tsala guda 10, kwamfutoci daban-daban, wayoyin hannu, firinta da dai sauran su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ekweremadu Bisa Zargin Safarar Sassan Jiki

Yan Sanda Sun Kwamushe Wasu Masu Satar Yara da Sunan Suna Kai Su Gidan Marayu

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun samu nasarar cafke wasu ɓata gari masu satat ƙananan yara.

Ɓata garin dai suna fakewa ne da kai yaran gidan marayu inda daga suke awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel