"Tsawalla Farashin Kaya Lokacin Ramadan Ya Saba Wa Koyarwar Addini", Nasihar Buhari Ga Yan Kasuwa

"Tsawalla Farashin Kaya Lokacin Ramadan Ya Saba Wa Koyarwar Addini", Nasihar Buhari Ga Yan Kasuwa

  • Shugaba Buhari ya taya al'ummar musulmi murnar zagayowar watan Ramadan tare da rokon su yi amfani da lokacin don komawa ga Allah
  • Shugaban ya kuma bayyana cewa karin farashin da yan kasuwa ke yi ya saba da shari'ar musulunci da al'adar watan Ramadan
  • Buhari bayyana haka a sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu, a sakon taya musulmi murnar zagayor watan Ramadan mai alfarma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce al'adar kara farashin kayan masarufi da yan kasuwa ke yi lokacin azumi ya saba da watan Ramadan.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da ya ke taya musulmi murnar zagayowar watan azumin Ramadan. Daily Trust ta rahoto.

A sakon fatan alheri don bikin fara gudanar da azumin wata mai alfarma na Ramadan, ya bukaci musulmai da su yi amfani da watan ''don aikata kyawawan ayyukan musulunci, da kuma gudun zunubi.''

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito

Shugaba Muhammadu Buhari
Tsawalla farashin kayan masarufi da wasu yan kasuwa ke yi lokacin ramadan ba daidai bane a addinance, Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon taya murnar shiga Ramadan da Buhari ya aike wa yan Najeriya

Shugaba Buhari, a wata sanarwa ta hannun mai taimaka a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya ce:

''Bari mu yi amfani da wannan damar don aikata kyawawan ayyukan koyarwar addinin musulunci, kamar kyautatawa da taimakon dan Adam.''
Shugaban ya cigaba da cewa, ''Wannan babbar dama ce ta komawa ga Allah da kuma gujewa shedancin da zai cutar da al'umma.''

Buhari ya ce:

''Ramadan lokaci ne da ake kauracewa ci da sha daga fitowar rana zuwa faduwarta, wanda ke janyo talaka da mai kudi su dandana irin yanayi guda, don karfafa alaka tsakanin ma su kudi da marasa kudi.''

Shugaba Buhari ya ce:

''A yayin da mu ka fara azumin kwana 30, mu tuna cewa Ramadan ba lokaci ne na kauracewa ci da sha kadai ba, lokaci ne na kauracewa duk wani shedanci da rashin kyautatawa da ke cutar da al'umma.

Kara karanta wannan

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya, bayani sun fito

''Ina sane da irin halayyar da wasu yan kasuwa ke yi na kara farashin kayan masarufi, ciki har da kayan abinci a farkon kowanne azumin Ramadan. Wannan halin ya saba da watan Ramadan da kuma shari'ar musulunci.''

Shugaba Buhari ya kara da cewa:

''Yayin gudanar da wannan muhimmiyar ibada a rayuwar musulmi, mu rabawa marasa karfi kayan abinci don su samu irin ni'imar da mu ke ciki, Allah ya na ninka ladan ayyukan alheri.''

Buhari ya sake nada Idris Musa shugabancin hukumar NOSDRA

A bangare guda, Idris Musa ya sake samun daman cigaba da shugabantar hukumar kiyayye kwararewar man fetur wato, NOSDRA.

Sanarwar hakan ya fito ne daga Ma'aikatar ta Muhalli ta kasa a ranar Litinin a shafinta na dandalin Twita (@FMEnvng).

Asali: Legit.ng

Online view pixel