Masu Garkuwa Sun Sace Yar Shekara 5 Da Matasa Biyu a Jihar Kwara

Masu Garkuwa Sun Sace Yar Shekara 5 Da Matasa Biyu a Jihar Kwara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sace mutane uku a wurare daban-daban a karamar hukumar Asa da ke jihar Kwara
  • Na farkon dai wani magidanaci mai suna Abdulfatai ne aka tare shi a mota ya tsere ya bar yaransa, sannan wani kuma aka tare su kan babur ya tsere ya bar yan mata biyu da ke masa aiki
  • Rundunar yan sandan jihar Kwara ta bakin mai magana da yawunta, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa an kama daya cikin wadanda ake zargin

Jihar Kwara - Yan bindiga sun sace wasu mutane uku a hare-hare daban-daban da suka kai a karamar hukumar Asa na jihar Kwara.

An tattaro cewa lamuran sun faru ne kusa da titin Aboto da Ajelanwa tsakanin karfe 2 da 6 na yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

Taswirar Jihar Kwara
Masu garkuwa sun sace mutane uku a Kwara. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin na farko ya faru ne lokacin da wani Abdulfatai, dillalin karafa ke hanyar dawowa daga gona tare da yayansa uku a cikin mota aka tare su.

Wata majiya daga unguwar ta ce:

"Abdulfatai ya tsere ya bar yaransa uku a cikin mota. Masu garkuwar sun saki kananan yaran biyu bayan sun ce za su gane hanyar zuwa gida sannan suka tafi da Abdulbasit wanda ya kai kimanin shekara biyar.
"Lamarin na biyu ya faru misalin karfe 6 lokacin da wani Saheed da aka fi sani da Bakayoko ke dauke da wani Ramat wanda ke koyon aiki da abokiyar aikinta kan babur kuma aka tare su.
"Amma Bakayoko ya yi kaman yana son ya dako takalminsa da ya fadi amma ya tsere ya bar matan biyu wadanda ke sanye da unifom din su."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa masu garkuwan sun tuntubi Abdulfatai, suna neman a biya su naira miliyan 10, don a sako dansa.

Martanin rundunar yan sanda

Mai magana da yawun yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce an kama daya cikin wadanda ake zargi.

Kalamansa:

"Eh, gaskiya ne kuma mun kama daya cikin masu garkuwar. Amma muna cigaba da bincike."

Amoketun ta kama wasu da kudaden bogi

A wani rahoton, jami'an hukumar tsaro na Amotekun sun cafke wani Celestine da takardun naira na bogi da suka kai N250,000.

Hakan na zuwa ne a lokacin da al'umma ke fama da karancin takardun naira a sassa daban-daban

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel