“Rayuwa Cikin Sauki”: Ma’aurata Sun Yi Aurensu a Saukake a Cikin Tsakar Gidansu

“Rayuwa Cikin Sauki”: Ma’aurata Sun Yi Aurensu a Saukake a Cikin Tsakar Gidansu

  • Wani bidiyon TikTok da ke nuna yadda aka yi shagalin bikin aure cikin sauki babu yabo babu fallasa ya haddasa cece-kuce
  • A yayin bikin, an gano amarya rike da kofin lemo inda ta duka a gaban masoyin nata cike da so da kauna
  • Mutumin ya yi mata kyautar kudi kamar yadda al'ada ta bukata kafin matashiyar ta gabatar da shi ga iyayenta

Wani dan gajeren bidiyo da ke nuna yadda ake shagalin bikin aure a tsakar wani gida ya haddasa cece-kuce.

A bidiyon wanda shafin @freeman.co ya wallafa, matar ta mikawa masoyin nata lemon kwalba a cikin kofi kafin ta gabatar da shi ga danginta.

Jama'a sun taru a wajen bikin aure
“Rayuwa Cikin Sauki”: Ma’aurata Sun Yi Aurensu a Saukake a Cikin Tsakar Gidansu Hoto: @freeman.co
Asali: TikTok

Shagalin bikin aure a saukake da yan uwa

Amaryar ta duka a gaban angon sannan ta gabatar masa da kofin. Bayan su dukka biyun sun sha lemon daga kofi daya, sai ya saka wasu kudade a ciki.

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Rabu Da Matarsa Saboda Gemu Ya Fito Mata, Hotunanta Na Da da Yanzu Sun Yadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashiyar ta rike hannunsa sannan ta gabatar da shi a gaban iyayenta yayin da suka durkusa don a sanya masu albarka. Mutane da dama sun jinjina masu kan yadda suka shirya auren a saukake.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

celenite ta ce:

"Rayuwar nan mai sauki ce, aure a saukake. Wasu mutane za su so burge mutanen karninsu. Allah ya albarkaci gidanku. Ina mai tayaku murna."

Real Max ta ce:

"Na tayaku mutna, ni ce ta gaba a kan layi."

user5338935203940 ta ce:

"An gode Allah akwai dattawa a wajen da suka gyara kuskuren baiwa yarinyar kofin ta mayar."

Jpoint clothes and fashion ta ce:

"Na tayaku murna Allah ya albarkaci aurenku."

Victoria oziomata ce:

"Na tayaku murna Allah ya yi mun irin naku."

mr fun ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

"Na tayaku murna, rayuwar aure mai nasara da gidan aure mai cike da farin ciki."

DIMMA ta ce:

"Na tayaki murna masoyiya, Allah ya albarkaci sabon gidanki."

Miji ya gudu ya bar mata saboda gemu ya fito mata a fuska

A wani labari na daban, wata mata ta shiga halin wayyo Allah bayan da mijinta ya rabu da ita saboda sauyawar halittarta inda gemu ya fito mata a fuska tamkar namiji.

Da farko matar ta shiga damuwa amma daga baya sai ta rungumi kaddararta domin haka Allah ya so ganinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel