'Yan Sanda Sun Cafke Masu Aikata Laifukan Zabe Da Dama a Jihar Kano

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Aikata Laifukan Zabe Da Dama a Jihar Kano

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano tayi kamen masu tayar da rikici a lokacin zaɓukan jihar da aka gudanar
  • Rundunar ta cafke mutane da dama bisa zargin aikata laifukan zaɓe daban-daban a lokacin da ake gudanar da zaɓen gwamna dana ƴan majalisar dokokin jihar
  • Daga cikin waɗanda ake zargi da tayar da rikicin har da ɗan majalisar dokokin jiha mai ci a yanzu

Jihar Kano- Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta cafke mutum 161 waɗanda suka aikata laifuka daban-daban a lokacin zaɓe.  Rahoton Channels Tv.

Daga cikin waɗanda aka cafken har da ɗan majalisar dokoki ta jiha mai wakiltar Gezawa, Isiaku Danja. Rahoton Vanguard.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Muhammad Gumel, shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Bayan Sake Komawa Kan Kujerar Sa, Gwamnan PDP Ya Sha Wani Babban Alwashi Kan Bola Tinubu

Rikici
'Yan Sanda Sun Cafke Masu Aikata Laifukan Zabe Da Dama a Jihar Kano Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Daga cikin laifukan da suka aikata sjn haɗa da satar akwatunan zaɓe, siyan ƙuri'u da kuma yunƙurin ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a jihar. An kuma kwato makamai da dama a hannun su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun cafke mutum 161 a lokacin zaɓe. An kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan satar akwatunan zaɓe, siyan ƙuri'u da kuma yunƙurin ƙona ofishin hukumar zaɓe." Inji shi
“A shirye muke wajen tabbatar da an gudanar da zaɓuka cikin lamuna ba tare da wani rikici ba. Ba za muyi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da cewa duk wanda yayi yunƙurin tayar da fitina ya fuskanci fushin hukuma."

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma nuna muhimman samun haɗin kai daga wajen jama'a domin tabbatar da nasarar zaɓen.

Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ayyana Zaben Wasu Mazabun Kano a Matsayin ‘Inconclusive’

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta (INEC) ta bayyana zaɓen wasu mazaɓu a jihar Kano, matsayin wanda bai kammalu ba.

Hukumar ta ayyana zaɓen ɗan majalisar dokokin jihar na ƙaramar hukumar Takai a matsayin wanda bai kammalu ba wato 'inconclusive'

Hukumar INEC ta zayyano dalilan ta na ɗaukar wannan hukuncin inda take cewa akwai lauje cikin naɗi a zaɓen. Ɗan takarar APC ne dai ya samu ƙuri'u mafiya yawa a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel