An Rasa Rayyuka 17 A Mummunan Hadarin Mota A Jihar Kano

An Rasa Rayyuka 17 A Mummunan Hadarin Mota A Jihar Kano

  • Akalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hadarin mota akan titin Wudil-Bauchi yayin da karin uku su ka ji rauni
  • Hadarin wanda ya hada da motoci biyu, kirara Honda da kuma Sharon ya faru a karamar hukumar Albasu da ke Kano da yammacin Laraba
  • Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta tabbatar da faruwar al'amarin, tare da tabbatar da bayar da gawarwakin ga iyalan mamatan da kuma kai wanda su ka ji rauni asibiti

Kano - Akalla mutane 17 ne aka ruwaito sun mutu yayin wasu mutum uku su ka ji rauni a wani hadarin mota a kauyen Yaura kan titin Wudil-Bauchi da ke karamar hukumar Albasu ta Jihar Kano.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura FRSC reshen jihar, Ibrahim Sallau Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

Hukumar FRSC
An Rasa Rayyuka 17 A Mummunan Hadarin Mota A Jihar Kano. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce hadarin ya rutsa da wata mota kirar Honda Accord dauke da lamba NSR 81 VW da kuma wata kirar karamar bas Volkswagen Sharon dauke da lamba NNG 275 XA da yammacin Laraba.

A cewarsa:

''Masu ababen hawan da ke wucewa ne su ka sanar da jami'anmu na sintiri da misalin 2:20 na rana, da samun rahoton, mun yi gaggawar tura jami'anmu wajen da abin ya faru don ceto wanda abin ya shafa da misalin 2:25 na rana."

Kwamandan FRSC na Kano ya bayyana sababin hadarin

Kwamandan ya kara da cewa ya hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa'a da kuma satar hannu ba bisa ka'ida ba wanda hakan ya janyo gaza sarrafa motar da ya yi silar hada karo, yayin da daya daga cikin motocin ta kama da wuta, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Majalisa da Aka Sace Ya Gudo, Ya Faɗi Abubuwan da Ya Gani a Sansanin 'Yan Bindiga

Kamar yadda ya ce:

''Hadarin ya hada da jimillar fasinjohi 21 cikin motocin biyun wanda 11 maza manya, mata biyar manya, da yaro namiji guda daya sun rasa rayukansu yayin da sauran ukun da su ka ji rauni sun kunshi namiji babba daya, mace babba daya, da yaro namiji daya."

Abdullahi ya ce an kai wanda su ka ji raunin zuwa babban asibitin Wudil don karbar magani, yayin da aka mika gawarwakin mamatan ga iyalan wanda hadarin ya shafa.

Kwamandan, wanda ya kai ziyara insa abin ya faru, ya shawarci ma su abin hawa da su bi dokokin tuki don kiyaye mutuwa barkatai da kuma raunuka.

Ya kuma jajantawa iyalan mamatan tare da rokon Allah ya jikan mamatan.

Motar yara yan firamari ya yi hadari a Legas

Bas wacce ke jigilar yara yan makarantar firamari ta yi kundunbala bayan hadari a unguwar Surulere a Legas a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: An yi mummunan hadari a jihar wata Arewa, mutane da yawa sun mutu, wasu sun raunata

Rahotanni sun nuna cewa dukkan yaran da ke motar da mai kula da su sun jikkata, shima direban ya yi rauni amma ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel