“Za Ki Iya Amsa Sunan Matar Aure?”: An Tilasta Amarya Yi Wa Dandazon Jama’a Girki, Bidiyon Ya Yadu

“Za Ki Iya Amsa Sunan Matar Aure?”: An Tilasta Amarya Yi Wa Dandazon Jama’a Girki, Bidiyon Ya Yadu

  • An sanya wata amarya tuka tuwo a bainar jama'a domin cika al’adun shagalin biki a ranar aurenta
  • A wani bidiyo da ya yadu, an gano kyakkyawar amaryar tsaye a cikin taron mata da dogon muciya a hannunta tana tuka tuwo babban tukunya
  • Amaryar wacce ke cike da farin ciki ta tuka tuwon cike da kwarewa lamarin da ya ba mata da dama mamaki inda suka yi ta jinjina mata

Wani hadadden bidiyo da aka yada a TikTok ya nuno wata amarya tana baje kolin girkinta a ranar aurenta.

Sanye da kayan aurenta, an garzaya da amaryar wajen girki don tabbatar da kwarewarta a bangaren aikin gida.

Amarya na tuka tuwo a taro
“Za Ki Iya Amsa Sunan Matar Aure?”: An Tilasta Amarya Yi Wa Dandazon Jama’a Girki, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @prettysummy054
Asali: TikTok

A bidiyon, ta tsaya a tsakanin sauran mata masu lura da ita domin tabbatar da ko ta iya aikin abinci.

An kuma bukaceta da ta tuka tuwo babban tukunya da aka ajiye a gabanta.

Kara karanta wannan

“Na San Yadda Yake Ji": Budurwa Ta Jizga Saurayinta a Bainar Jama’a, Ta Karbe Wayar Da Ta Siya Masa a Bidiyo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan shine zai cika al’addu da ake gudanarwa yayin shagulgulan bikin aure. Ta karbi muciyan sannan ga mamakin mutanen da suka hallara a wajen, sai ga shi tana tuka tuwon cike da kwarewa har sai da sauran matan suka yi ihu da jinjina ma kokarinta.

Bidiyon ya haifar da martani da dama daga jama’a wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu kan wannan al’ada ta aure.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Big-Ola ta ce:

"Zan fadi taliya kawai na iya girkawa."

@Marah ta rubuta:

"Mijina rufe ido kawai zai yi don zan ba da kunya wannan muciyan ya fi karfin hannuna."

@Hamdiya Inusahta ce:

"Ba zan yi ba idan basu yarda na iya girki ba su kyale kawai."

@Z. ta yi martani:

"Ni ce nan ina kokarin tabbatarwa mai shirin zama mijina a gaba cewa ni tasa ce."

Kara karanta wannan

"Na Taki Sa'ar NYSC": Budurwa Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

@Avans Gloria ta yi martani:

"Wato haka zan ba dangin mijina kunya...kunu kawai na iya damawa."

@Zara Chiza Okere ta yi martani:

"Taliya kawai na iya girkawa hakan na nufin za su hadu su yi mani duka a wannan ranar."

Yan mata sanye da hijabi sun sha rawa a wajen biki, bidiyon ya kayatar

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu yan mata biyu cikin shiga ta kamala sun kayatar da jama'a a wajen wani biki bayan sun nuna kwarewarsu a bangaren rawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel