“Kyawawa Da Su”: Yadda Yan Mata Musulmai 2 Suka Girgije a Wajen Biki, Bidiyon Ya Yadu

“Kyawawa Da Su”: Yadda Yan Mata Musulmai 2 Suka Girgije a Wajen Biki, Bidiyon Ya Yadu

  • Wasu yan mata Musulmai biyu sun dauka hankali bayan bidiyonsu suna tikar rawa a wajen wani biki ya yadu a soshiyal midiya
  • Yan matan cikin shiga ta dogayen riguna da hijabai sun isa filin rawa inda suka girgije cikin taku iri daya
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjinawa yanayin shigarsu ta kamala yayin da suka kimanta takun yan matan biyu

Wasu yan mata musulmai biyu sun kayatar da mutane da yanayin rawarsu a wajen wani shagalin bikin aure.

Yanayin irin rawar da suka taka a wajen bikin wanda shafin @teamdfams ya wallafa a TikTok ya haifar da martani da dama.

Yan mata suna tikar rawa sanye da hijabi
“Kyawawa Da Su”: Yadda Yan Mata Musulmai 2 Suka Girgije a Wajen Biki, Bidiyon Ya Dauka Hankali Hoto: @teamdfams
Asali: TikTok

Da suke isa filin taron, yan matan sanye da dogayen riguna, hijabai da takalma masu tsini sun taka rawar wata waka da ke tashi a dakin taron cikin salo mai daukar hankali.

Kara karanta wannan

"Ya Yi Wuff Da Tsaleliyar Budurwa": Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Ya Wuff Da Kyakkyawar Yarinya Ya Haddasa Cece-Kuce

Duk da dogayen tufafin da suka saka, an gano yadda yan matan ke jefa kafafuwa da girgije jikinsu wanda ya yi daidai da sautin kidan da ke tashi, kuma hakan ya burge mahalarta taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu amfani da soshiyal midiya ya kimanta rawan yan matan, inda da dama suka jinjinawa yanayin shigarsu ta kamala.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Alagbada Temiloluwa Bejideya ce:

"Na kasa gajiya da kallon yadda kyawawan yan matan nan masu shiga ta kamala suke."

B yusrah ta ce:

"Dan Allah menene amfani rufe kai bayan duk wannan rawa da suka tika."

Jaysamuels01 ya ce:

"Abun da hakan ke nufi za ka iya rufe jiki kuma ka isar da sakon da ake so."

donatusiruoma ta ce:

"Kamala dangane da aji."

issaabdullateef ya ce:

"Tsawonsu ne ya dauki hankalina."

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Ki Sakin Ma'aurata Da Diyarsu Bayan Karbar N2m Kudin Fansa, Sun Sake Gabatar Da Wata Bukatar

Vivian Olachi ChIma ta ce:

"Na so su, yan mata ba sai kun fallasa jikinku don tabbatar da shirme ba...kalli wadannan kyawawan yan matan da takalma masu tsini kuma sun kayatar sosai."

Oluwo na Iwo ya samu karuwa da amaryarsa yar Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya albarkaci babban basaraken kasar Yarbawa, Oluwo na Iwo da amaryarsa bakanuwa da samun zuri'a a tsakaninsu.

Basaraken ne ya sanar da wannan labari a shafinsa na soshiyal midiya yayin da yake nuna farin ciki da godiyarsa ga Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng