“Yana Da Nutsuwa”: Budurwa Ta Karbe Waya Da Bell Da Ta Siyawa Saurayinta a Bidiyo

“Yana Da Nutsuwa”: Budurwa Ta Karbe Waya Da Bell Da Ta Siyawa Saurayinta a Bidiyo

  • Wata budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuke a taron jama’a yayin da ta kunyata saurayinta bayan ta gan shi tare da wata mace
  • Ta fara gaura mashi mari tana mai kiransa da karuwan namiji sannan ta raba shi da wani abu da ta siya mai
  • Fusatacciyar budurwar ta sa shi cire bel din wandonsa da ta siya masa a wajen sannan ta karbe wayarsa, lamarin da ya ba mutane mamaki

Wani mutum ya shawarci maza da kada su kuskure su yarda mace ta ciyar da su yayin a ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda budurwa ta kunyata saurayinta a bainar jama’a.

Matashiyar, wacce ta yi magana da Yarbanci, ta ga saurayinta da wata mace sannan ta kira shi da karuwan namiji yayin da ta zarge shi da cin amanarta.

Kara karanta wannan

"Na Taki Sa'ar NYSC": Budurwa Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

Budurwa tana jizga saurayinta a bainar jama'a
“Yana Da Nutsuwa”: Budurwa Ta Kabe Waya Da Bell Da Ta Siyawa Saurayinta a Bidiyo Hoto: @olasugar23
Asali: TikTok

Nan take ta dauke shi da mari a fuska kafin ta umurce shi da ya dawo da duk wani abu da ta siya masa.

Ta karbe bel din wandonsa da wayar hannunsa yayin da budurwar da ake zargin yana cin amana da ita ta kira shi yaya tana mai tambayar abun da ke faruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin ya yi shiru abinsa yayin da ake cin mutuncinsa a bainar jama’a sannan ya dauke kanwarsa daga wajen.

Mutanen da ke wajen sun gano cewa macen da budurwar tasa ta yi tunanin yana cin amana da ita kanwarsa ce.

Bidiyon TikTok din ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Mo6 ya ce:

"Na ji masa bakin ciki a matsayina na namiji ganin ana yiwa wani namijin cin kashi ba tare da mutuntawa ba saboda ba zai iya daukar dawainiyar kansa na yau da kullun ba."

Kara karanta wannan

"Ya Yi Wuff Da Tsaleliyar Budurwa": Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Ya Wuff Da Kyakkyawar Yarinya Ya Haddasa Cece-Kuce

e ya ce:

"Ku da kuke cewa yarinyar muguwa ce.
"Amma idan namijin ne ya aikata hakan yanzu fa.
"Mahaukata za su dunga ihun"Dan uwa muna alfahari da kai."

user2178443511276 ya ce:

"Baaba, nutsuwar gayen 100% ne wato bi ma'anaa....
"Na ji radadinsa a lokacin. Kada ka bari mace ta ciyar da kai."

Lol ta ce:

"Na ga mutuncin kanwar saboda a matsayina na mace babu wanda zai iya yi wa dan uwana haka a gabana."

Magidanci ya yi wuff da kyakkyawar budurwa, bidiyon budar kansu ya haddasa cece-kuce

A wani labari na daban, jama'a a soshiyal midiya sun caaa a kan wani ango bayan ganin bidiyon aurensu da tsalalliyar amaryarsa, suna ganin ya yi mata wayo saboda tazarar shekarun da ke tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng