Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace Sama da 60 a Neja

Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace Sama da 60 a Neja

  • Wasu miyagu sun kashe mutane uku cikinsu har da Basarake a sabon harin da suka kai kauyukan kananan hukumomi 2 a jihar Neja
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kwashe awanni suna aikata manufarsu, kuma sun yi awon gaba da wasu mutane 70
  • Har yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar yan sanda ko gwamnatin jihar Neja game da sabon harin

Niger - Mutane uku ciki har da Magajin gari sun rasa rayukansu yayin da aka sace wasu 70 a wasu ƙauyukan kananam hukumomin Munya da Paikoro, jihar Neja.

The Nation ta ce Basaraken garin Beni na cikin waɗanda aka kashe, haka nan an kashe ɗan Magajin Garin Kwagana da kuma wani bawan Allah a kauyen Adunu, ƙaramar hukumar Paikoro.

Harin yan bindiga.
Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace Sama da 60 a Neja Hoto: thenation
Asali: Twitter

A cewar wani mazaunin Adunu, John Lazarus, 'yan bindigan sun fara aikata wannan ɗanyen aikin ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

Ya ce tun daga wannan lokacin suka tsare mutanen ƙauyukan har zuwa ƙarfe 3:00 na rana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya kara da cewa da yawan mutane a Daji suka kwana tsawon daren nan saboda tsoron kar 'yan bindigan su sake kaddamar da wani harin idan sun koma gida.

Sakamakon haka, Mista John Lazarus ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a Najeriya su taimaka su kawo masu ɗauki.

Lazarus ya yi ikirarin cewa yan ta'adda sun ƙara matsawa wajen kai hare-hare kan mutane a tsawon watanni uku na baya-bayan nan amma ga dukkan alamu gwamnati ba ta ɗaukar wani matakin a zo a gani.

Har kawo yanzun kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Emmanuel Umar, da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda ba su ce komai ba game da sabon harin.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, Sarkin Kano Ya Fito Fili Ya Gayawa Mutanen Jihar Abinda Yakamata Su Yi a Zaben Gwamna

Najeriya ya koma ta 36 a duniya

A wani labarin kuma Rundunar Sojin Najeriya Ta Ka Matsayi Na 36 Daga Cikin 145 Mafi Karfin Wuta a Duniya

Najeriya ta yi ƙasa da mataki ɗaya a jerin kasashe 145 ma su karfin soji a faɗin duniya, haka nan ta ƙara samun koma baya a jerin kasahen Afirka.

Ƙasar Amurka ce a matakin farko sai kum Rasha da ke mara mata baya, a Afirka kuma ƙasar Masar ce ke jan ragama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel