Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta dage fara aikin kidiya yan kasa na shekarar 2023 da aka yi shirin farawa a watan Maris zuwa Mayu
  • Alhaji Lai Mohammmed, Ministan Labarai da Al'adu na kasa ne ya bayyana hakan a yau Laraba 15 ga watan Maris bayan taron FEC
  • Mohammed ya ce an dage kidayar jama’a ne saboda sauya jadawalin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha zuwa ranar 18 ga Maris

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta matsar da fara yin aikin kidaya yan kasa na shekarar 2023 zuwa watan Mayun 2023.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, a ranar Laraba, ya bayyana hakan a Abuja bayan taron majalisar zartarwa wato FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Lai Mohammed
Lai Mohammed ya ce an dage yin kidaya zuwa watan Mayu. Hoto: Ma'aikatar Labarai da Al'adu na Najeriya.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da farashin kayayyaki ya kara hawa a Najeriya daidai karancin Naira

A cewarsa, za a yi kidayar a watan Mayu.

A baya, The Punch ta rahoto cewa za a fara kidayar a ranar 29 ga watan Maris.

Abin da ya sa aka dage yin kidayar ta shekarar 2023 - Lai Mohammed

Ministan ya ce ya zama dole a dage fara aikin kidayar ne saboda sauya ranar yin zabukan gwamnonin jihohi zuwa ranar 18 ga watan Maris.

Mohammed ya ce majalisar zartaswar ta amince a ware naira biliyan 2.8 ga Hukumar Kidayar ta Kasa, NPC, domin ta siyo wasu manhajoji da za a yi amfani da su wurin aikin.

Ya ce:

"Akwai takardar da Hukumar Kidaya ta Kasa ta gabatar na neman siyan wasu manhajoji da za su yi amfani da su wurin kidayar a watan Mayun wannan shekarar. Na yi imanin cewa saboda sauya ranar zabe, ba za su iya fara kidayar kamar yadda aka shirya ba a farko.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi 15 Da PDP Ka Iya Yin Nasara a Zaben Ranar Asabar

"Sun nemi izinin majalisar a bada kwangilar siyo manhajar kidiyar kan kudi naira biliyan 2.8."

Wannan shine kidayar da za a yi bayan shekaru 17 a kasar.

Daily Trust ta rahoto cewa wani ma'aikacin hukumar NPC, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da dage fara aikin kidayar.

Ya ce:

"Yanzu za a fara aikin kidayar daga ranar 3 zuwa 7 na watan Mayu kuma shine abin da aka mika wa Shugaban Kasa. Zai amince da hakan amma bai riga ya sa hannu ba."

Shugaba Buhari ya rantsar da mutum 7 da ya ba wa mukami

A wani rahoton kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da wasu mutane bakwai da ya sabunta nadinsu a matsayin mambobi na majalisar gudanarwa na hukumar ICPC mai yaki da cin hanci.

Buhari Sallau, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel