Gwamna Masari Ya Sake Korar Masu Rike Da Mukaman Gwamnati 3 A Katsina

Gwamna Masari Ya Sake Korar Masu Rike Da Mukaman Gwamnati 3 A Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sake korar wasu manyan ma'aikatan gwamnatinsa gabanin zaben gwamna
  • Cikin wadanda aka kora akwai Alhaji Bilyaminu Mohammed Rimi, shugaban hukumar sufuri da Hajiya Amina Lawal Dauda, mashawarciya na musamman kan harkokin mata
  • Ana yi wa wannan korar da sauye-sauyen kallon wani mataki da gwamnan ke dauka don korar wadanda suka yi wa APC zagon kasa a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu

Jihar Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sake korar wasu ma'aikata a wani mataki da ake kallon yana yaki da masu zagon kasa ne cikin gwamnatinsa, rahoton Tribune.

Alhaji Bilyaminu Mohammed Rimi, shugaban hukumar sufuri ta jihar da Hajiya Amina Lawal Dauda, mashawarciya ta musamman kan yaya mata suna cikin wadanda aka sallama.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi: Duk da Yana PDP, Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Ayyana Goyon Baya Ga Dan Takarar APC

Gwamna Masari
Gwamna Masari ya sallami mutane 3 daga gwamnatinsa. Hoto: Katsina Post
Asali: Twitter

Hakazalika, an sallami tsohon ciyaman din jam'iyyar APC na jihar, Alhaji Shitu Shitu daga kumaninsa na mamba na kwamitin hukumar aikin hajji na jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal ya fitar ta Alhaji Abubakar Darma ya maye gurbin Shitu Shitu a hukumar alhazai yayin da wata sanarwar ta ce Alhaji Gambo Abdulkadir Rimi shine sabon shugaban kwamitin KTSTA da ya maye gurbin Bilyaminu Rimi.

Gwamna Masari ya nada Magajin Garin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir a matsayin ciyaman din kwamitin hukumar aikin hajji ya maye gurbin Alhaji Yusuf Barmo da aka kora a baya.

Har wa yau, gwamnan ya tura Alhaji Usman Nadada, kwamishinan kasa da sufiyo zuwa ma'aikatar ayyuka na musamman yayin da Bishir Gambo Saulawa aka dauke shi daga Ma'aikatar Wasanni da Cigaban Al'umma zuwa Ma'aikatar Kasa da Sufiyo.

Kara karanta wannan

Fada Ya Kaure Tsakanin Yan Daban APC da PDP, An Yi Kisa a Jihar Arewa, Da Dama Sun Jikkata

Masari ya kuma nada na hannun damansa, Sani Danlami a matsayin Kwamishinan Wasanni bayan ya gaza cin nasarar komawa majalisar tarayya don wakiltar Katsina.

Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta karrama Gwamna Masari da lambar yabo na 'Abokin Coci'

A baya, kun ji cewa kungiyar kiristocin Najeriya wato CAN ta ba wa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina lambar yabo na 'Abokin Coci'.

Kungiyar ta CAN ta ce ta ba wa Masari lambar yabon ne saboda ayyukan alheri da raya kasa da ke yi a jihar da kuma al'ummar kirista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel