INEC Zata Ɗaukaka Ƙara Kan Umurnin Kotu Na Ayi Zaɓe Da TVC

INEC Zata Ɗaukaka Ƙara Kan Umurnin Kotu Na Ayi Zaɓe Da TVC

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bata amince da hukuncin da wata kotu tayi ba kan yin zaɓe da katin zaɓe na wucin gadi
  • INEC ta ce sam bata amince ba sannan zata ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba domin ƙalubalantar hukuncin
  • Wata babbar kotun tarayya dai ta umurci hukumar INEC da ta bari wasu mutum biyu su hi zaɓe da katin zaɓe na wucin gadi

Abuja- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), zata garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin wata babbar kotun tarayya, da ya umurce ta da ta bari wasu mutum biyu su yi zaɓe da katin zaɓe na wucin gadi (TVC).

Rotimi Oyekanmi, kakakin shugaban hukumar INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana a cikin ƴar gajeruwar sanarwa cewa an ba hukumar kwafin hukuncin kotun. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

2023: Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Kotu Ta Jiƙawa INEC Aiki, Ta Bata Wani Sabon Umurnin Dole

Shugaban INEC
INEC Zata Ɗaukaka Ƙara Kan Umurnin Kotu Na Ayi Zaɓe Da TVC Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Sai dai, ya ƙara da cewa hukumar zata ɗaukaka ƙara kan wannan hukuncin. Rahoton Guardian

“Hukumar INEC na ɗaukar matakan da suka dace domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun." Inji shi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun shekarar 2019, INEC ta sha nanata cewa masu rajistar zaɓe waɗanda suke da katin zaɓen su na din-din-din (PVC) ne kawai ke da hurumin kaɗa ƙuri'un su a rumfunan zaɓe a ranar zaɓe.

Amma a ranar Alhamis, wata babbar kotun tarayya, a birnin tarayya Abuja, ta yanke wani hukunci saɓanin matsayar ta hukumar INEC.

Kotun ta yanke hukunci ne kan ƙarar da wasu mutum biyu suka shigar da hukumar INEC, inda ta umurci INEC da ta bar mutum biyu su yi zaɓe da katin zaɓen su na wucin gadi a zaɓukan 2023.

Alƙalin kotun, Obiora Egwuatu, ya yanke hukuncin cewa dole a bar mutum biyun da suka shigar da ƙara su yi zaɓe, tun da akwai bayanan su a cikin rajistar masu zaɓe ta INEC, sannan an basu katin zaɓe na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Mamaye Ni Aka Lalube Min Wayoyi Na a Wajen Karɓar Satifiket Ɗin lashe Zaɓe, Sanatan APC

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

A wani labarin na daban kuma, shugaban majalisar wakilai ta Najeriya yana harin wani muƙami mai gwaɓi a kusa da Tinubu.

Shugaban majalisar dai ya ƙi zuwa ya karɓi satifiket ɗin sa a hannun INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel