Mutum 6 Sun Mutu, An Yi Garkuwa Da Waso 50 Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Hari Jihar Neja

Mutum 6 Sun Mutu, An Yi Garkuwa Da Waso 50 Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Hari Jihar Neja

  • Tsagerun yan bindiga sun kai kazamin hari kan wasu garuruwa a kananan hukumomin Rafi da Wushishi na jihar Neja
  • Maharan da suka yi zazzafan arangama da jami'an rundunar sojoji sun halaka mutum shida harda wata mai juna biyu
  • Rahotanni sun kawo cewa yayin harin da ke zuwa yan kwanaki kafin zabe, yan bindigar sun yi garkuwa da mutane kimanin su 50

Niger - Channels TV ta rahoto cewa yan bindiga sun halaka mutum shida sannan suka yi garkuwa da wasu 50 a kananan hukumomin Rafi da Wushishi da ke jihar Neja.

Majiyoyi sun ce mutanen sun mutu ne bayan musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an sojoji da yan bindigar, kuma hakan ya yi sanadiyar da wasu da dama suka jikkata.

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello yana jawabi
Mutum 6 Sun Mutu, An Yi Garkuwa Da Waso 50 Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Hari Jihar Neja Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Wani mazaunin wani kauye a karamar hukumar Rafi wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya fada ma Channels TV cewa daga cikin mutum shida da aka kashe harda wata mata mai cikin watanni 6.

Kara karanta wannan

Saura Kwanaki Zabe: Gwamnan Kano Ya Yi Wa Mutane 12 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Afuwa

Mazauna kauyukan sun nuna kaduwarsu kan dalilin da yasa harin ke zuwa yan kwanaki kafin zabukan gwamnoni da yan majalisun jihohi a kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani lamari makamancin haka ya gudana yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya a karamar hukumar Mariga ta jihar.

Kwamishinan tsaro na jihar Neja ya yi martani

Da yake tabbatar da harin baya-bayan nan, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin agaji, Mista Emmanuel Umar, ya ce har yanzu basu tabbatar da adadin mutane da suka mutu ba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati bata yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawar da duk wasu miyagu a jihar.

An tattaro cewa yan bindigar sun addabi al'ummar yankin Anawanka, Sabon Gari da Kundu a kananan hukumomin biyu.

An kuma rahoto cewa rundunar sojin saman Najeriya ta fafata da yan bindigar na tsawon awanni amma babu cikakken bayani game da aiki, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An Kashe Mutane 50, An Raunata Da Dama, An Kona Gidaje Yayin Hare-Hare A Binuwai

Ba za mu yarda kashe-kashen rashin hankali ba a Najeriya, Tinubu

A wani labarin kuma, zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai kan hare-haren da yan bindiga suka kai jihohin Zamfara da Kano a baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar Hakimi a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel