Ganduje Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 12 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa

Ganduje Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 12 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi afuwa ga wasu mutane 12 da aka yanke wa hukuncin kisa a gidan gyara hali
  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya kuma yi wa wasu mutum shida sassauci daga hukuncin kisa zuwa na daurin rai da rai
  • Fursunonin sun samu wannan garabasa ne bayan nuna kyawawan halayya yayin da suke zaman jiran hukunci a gidan gyara halin

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa wasu fursunoni 12 da aka yankewa hukuncin kisa afuwa.

Har ila yau, Daily Trust ta rahoto cewa Ganduje ya kuma mayar da hukuncin kisa da aka yankewa wasu mutum shida zuwa daurin rai da rai.

Gwamna Abdullahi Ganduje yana jawabi
Ganduje Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 12 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar ta rahoto a wata hira da ta yi da shi a 2021, Ganduje ya bayyana cewa gwamnoni na tsoron sanya hannu a hukuncin kisa saboda basa so su yi izinin aiwatar da shi sannan daga baya a gano mai shi bai cancanci mutuwa ba.

Kara karanta wannan

Kwana 4 Gabanin Zabe, Kotun Ƙoli Ta Ayyana Halastaccen Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jiha 1

Dalilin yi wa fursunonin afuwa

Wata sanarwa da kakakin hukumar gyara hali na Najeriya a Kano, SC Musbahu Lawan Nassarawa, ya saki a ranar Talata, 7 ga watan Maris, ya ce gwamnan ya kuma yi wa wasu mata hudu afuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ganduje ya yi wa matan wadanda aka yankewa wa'adi mai tsawo afuwa ne bayan hukumar gidan gyara halin ta bayar da shawarar haka duba ga kyawawan dabi'unsu.

Gwamnan ya kuma baiwa kowannensu kudin mota N5,000 domin su samu damar isa ga iyalansu, rahoton Vanguard.

An yi jan hankali ga fursunonin da aka yi wa afuwa

Nassarawa ya ce shugaban kwamitin jin kai, Abdullahi Garba Rano, da shugaban hukumar gidan gyara hali reshen jihar Kano, Sulaiman Mohd Inuwa, sun yi godiya ga gwamnan.

Sun jijina masa kan amfani da ikon da kundin tsari ya bashi wajen sakin fursunonin da suka nuna kyawawan halayya bisa aiki da shawarar kwamitin da hukumar gidan yari.

Kara karanta wannan

An Tsinci Wani Mutum Da Aka Yi Wa Fashin N97,000 A Sume A Gefen Titi Da Kebur A wuyansa A Jigawa

Inuwa ya yi kira ga fursunonin da aka saki da su zamo jakadun kirki na hukumar gidan gyara hali na Najeriya da jama'a sannan su guji sake aikata laifi.

A cewar sanarwar, wasu daga cikin fursunonin da aka yi wa afuwa sun shafe tsawon shekaru 25 suna jiran hukunci.

Hatsarin mota ya yi ajalin yan uwan juna su 10 a hanyar dawowa daga biki a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar rasa ran wasu mutane 10 yan gida daya a hanyarsu da komawa Kachia da ke jihar Kaduna bayan sun halarci biki a Kano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel