Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Yan Boko Haram Sama Da 200 a Borno

Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Yan Boko Haram Sama Da 200 a Borno

  • Rigimar dake tsakanin kungiyoyin ta'addan Najeriya ta ki ci, ta ki cinyewa har ila yau
  • Rahoto a ranar Asabar ya nuna yadda aka kashe daruruwan yan Boko Haram a shara guda
  • Rundunar Operation Hadin Kai ta bayyana irin nasarorin da take samu a yankin arewa maos gabas

Borno - Yan ta'addan ISWAP sun hallaka yan ta'addan Boko Haram akalla 200 a mumunar artabun da suka yi a Arewa maso gabashin Gudumbali, jihar Bornon Najeriya.

Wadanda aka kashe sun hada da mayaka, mata da yara, rahoton ZagaZola.

An tattaro cewa yan ISWAP sun kaiwa yan Boko Haram harin kwantan bauna ne a kauyen Choliye.

Majiyoyin sun bayyana cewa hakan yasa yan ta'addan na Boko Haram suka arce zuwa tsaunin Mandara dake yankin Gwoza, yayinda wasu suka gudu Konduga, Mafa, Dikwa, Gajiram da yankunan tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

Harin Chadi
Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Yan Boko Haram Sama Da 200 a Borno Hoto: Yaki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Manyan jagororin Boko Haram da suka tsallake rijiya da baya a harin sun hada da Kwamandan Mantari da Maimusari, Abbah Tukur; Kwamandan Mgauri, Abu Isa; sabon kwamandan Garin Abu Ikliima, Alhaji Ali Hajja Fusami, da Abu Ali, dss.

A cewar majiyar:

"A Yale, wani kauye dake karamar hukumar Konduga, kwamandan ISWAP Modu Bashir Okocha, ya jagoranci runduna domin kai wani wajen yan Boko Haram kuma ya kashe mutum 15 cikinsu, tare da kwace babura da makamai."
"Wadannan hare-hare ya tilasta daruruwan yan Boko Haram tare da iyalansu mika wuya ga rundunar Sojojin Operation Hadin Kai a Mafa, Konduga da sauran filayen daga. Waus sun gudu Mafa ta Dikwa da kuma Nijar. ta tafkin Chadi."
"Wasu mayakan sun gudu sansanin Bakura Wulgi, wanda aka fi sani da Abou Oumaymah, a yankin Marte da Krenowa yayinda wasu suka gudu tsaunin Mandara dake Gwoza domin neman taimako daga wajen Ali Ngulde."

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayi 50 da Suka Sace Kaya a Gobarar Kasuwar Maiduguri.

Rikicin da ya barke yan Boko Haram da ISWAP ya ta'azara kuma har yanzu sun gaza sulhu tsakanin juna.

Sun kaiwa juna hare-hare a baya

A ranar 6 ga Disamba, 2022, yan Boko Haram sun kai mumunan hari inda suka hallaka matan yan ta'addan ISWAP 33 a dajin Sambisa.

A ranar 31, yan Boko Haram suka sake kai hari wa ISWAP a Toumbum Allura Kurnawa da Kangar.

Wannan ne dalilin da ya sa kwamandan ISWAP Abu Mus'ab Albarnawi ya gudu Somalia, Mali da Chadi domin neman dauki daga wajen abokansu gudun kada daularsa ta fadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel