Peter Obi Ya Lallasa Tinubu, Atiku da Kwankwaso A Birnin Tarayya Abuja

Peter Obi Ya Lallasa Tinubu, Atiku da Kwankwaso A Birnin Tarayya Abuja

  • Tsohon gwamna Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ya zama zakaan gwajin dafi a siyasar Najeriya
  • Ya yiwa Asiwaju Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP babban lahani a zaben dake gudana
  • Har yanzu ana cigaba da tattaro sakamakon zabe daga kananan hukumomi da jihohi a fadin tarayya

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Gregory Obi, ya samu nasara a zaben babbar birnin tarayya FCT Abuja.

Nasarar Obi ta bayyana ne bayan kammala kirgen kuri'u a manyan hukumomin Abuja guda shida, rahoton TheCable.

Ya lallasa Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP.

Zaku tun cewa jam'iyyar PDP ce ta shahara da lashe zabe a Abuja, amma wannan karon na uku ta zo.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Karbe Jihar Ribas Daga Hannun Atiku Da Peter Obi

peter
Peter Obi Ya Lallasa Tinubu, Atiku da Kwankwaso A Birnin Tarayya Abuja
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga Sakamakon:

APC: 90,902

PDP: 74,199

LP: 281,717

NNPP: 13,247

Adadin wadanda aka tantance: 478923

Halastattun kuri'u: 460080

Kuri'un da aka watsar: 18581

Ga yadda zaben ya kaya a kananan hukumomi Abuja

1. Gwagwalada Area Council

APC— 15890

LP— 19,694

NNPP— 483

PDP— 10987

2. Bwari Area Council

APC 13156

LP 67,198

NNPP 877

PDP 10835

3. Kuje Area Council

APC 10648

LP 14,257

NNPP 266

PDP 10028

4. Abaji Area Council

APC 10370

LP 2874

NNPP 104

PDP 6888

5. Kwali Area Council

APC 11,242

LP 7,302

NNPP 324

PDP 9,054

6. AMAC

APC 29596

LP 170392

PDP 26407

Lalong Ya Gaza Samun Nasarar Kujerar Sanata Da Ya Nema

Babban Darakta janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima kuma gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong shima yasha ƙasa a ƙoƙarin sa na zuwa majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dan El-Rufai Ya Kayar Da PDP, NNPP Da Sauran Yan Takara, Ya Lashe Kujerar Majalisar Tarayya

Lalong yasha kayi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP mai suna Napoleon Bali.

Jaridar Vanguard ta ambato cewa Lalong yayi takara a cikin inuwar jam'iyyar APC kuma ya samu ƙuria guda 91, 674, yayin da Bali wanda yayi nasara ya samu ƙuri'u 148,844.

Idan dai za'a iya tunawa, tun a tashin farko me dai, Lalong ya rasa akwatin sa dake Ajikamai ga jam'iyyar Labor Party da kuma Shendam ta tazara mai matuƙar yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel