Ma'aikatan Wucin Gadin INEC Sunyi Ƙemadagas Baza Suyi Aikin Zaɓe ba Har Sai An Basu kuɗin Somin-taɓin Tukuna

Ma'aikatan Wucin Gadin INEC Sunyi Ƙemadagas Baza Suyi Aikin Zaɓe ba Har Sai An Basu kuɗin Somin-taɓin Tukuna

  • Abisa Ka'ida Ana Bada Kudin Somin-Tabi Ga Ma'aikatan Na Wucin Gadi Domin Shiryawa Halin Ujilar Ciki da Bakin salati
  • Ma'aikatan Sun Zargin Basuji Dumus ba, saboda Haka Bazasuyi Aiki ba A Wani Salo na "Ba Kudi, Ba Aiki".
  • Hakan Na Zuwa Ne a Lokacin da Akwatuna Da Yawa Tuni Sukayi Nisa Da Kada Kuri'unsu

Kano - A yayin da ake tsaka da hada-hadar zaɓuka lungu da saƙo na ƙasar nan, wata sabuwar balahira ta taso daga mazaɓar Kwankwaso.

Balahirar ta samo asali ne a Mazaɓar dake garin Kwankwaso ta Madobin Kano dake Arewacin Najeriya.

Wasu ma'aikata ne suka bijire tare dayin burki suka nannaɗe hannayen su suna mazurai. Koda aka tambaye su me yasa basu soma aikin su ba, duba da sauran wurare tuni sunyi nisa.

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe: Jam'iyyar APC ta Dakatar da Babban Yayan Gwamna Sani Bello

Kwankwaso
Ma'aikatan Wucin Gadi na INEC Sunyi Ƙemadagas Baza Suyi Aikin Zaɓe ba Har Sai An Basu kuɗin Somin-taɓin Tukuna Hoto: ~Y. Mukhtar
Asali: Original

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai suka bayyanawa cewar, su basuji dumus na dage kuɗin somin-taɓi da INEC take bawa ma'aikata ba domin karin kumallo.

Sabili da haka ne, suka ce ba zasuyi aiki ba.

Kamar yadda suka shaidawa wakilan mu na zazu da suke wuraren gudanar da zaɓuɓɓukan, sunce atafau bazasuyi aiki ba idan har ba'a basu kuɗin da aka tanadar musu ba domin gudanar da aikin cikin jin daɗi da walwala.

Legit ta ruwaito cewa, har yanzu akwai akwatina bila adadin da ba'a soma kaɗa ƙuri'a ba saboda irin wannan tasgaro da ake fuskanta.

A wani labari mai kama da wannan kuma an ruwaito cewar:

Buhari Ya Nunawa Jama'a Kuri'arsa

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari tare da uwargidarsa, Aisha Muhammadu Buhari suka kada kuri'arsu, Buhari idan za'a iya tunawa dira a mazabarsu dake garin Daura, jihar Katsina da sanyin safiyar Asabar. Shugaban bayan kada kuri'arsa ya yi hira da manema labarai da suka yi masa tambayoyi kuma ya bada amsar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel