Zabe Ya Gabato, IGP ya yi Mamaya da Wasu Sauye-sauyen Kwamishinoni a Manyan Jihohi

Zabe Ya Gabato, IGP ya yi Mamaya da Wasu Sauye-sauyen Kwamishinoni a Manyan Jihohi

  • Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya ya tura sababbin Kwamishinoni hudu domin su kula da zaben jihar Ribas
  • SP Grace Iringe ta ce Shi kuma CP CP Okon O. Effiong ya tashi daga Fatakwal, zai yi aikin zabe a Enugu
  • Abdullahi Haruna Kiyawa wanda shi ne Kakakin ‘yan sandan Kano, ya ce sun yi sabon Kwamishina

Abuja - A yayin da zaben shugaban kasa ya karaso a Najeriya, ana ta yin wasu tsare-tsare da za su tabbatar mutane sun yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Daily Trust ta ce Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya ya tura mataimakinsa mai kula da shiyya ta 13 da ke Awka a jihar Anambra zuwa Ribas domin aikin zabe.

AIG Abutu Yaro zai lura da Kwamishinonin ‘yan sanda hudu da aka tura saboda shirin zabe.

Babbar jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta ce Kwamishinonin da aka aiko zuwa reshen sun hada da Yomi Olanrewaju.

Kara karanta wannan

An Dankara ‘Yan Sanda Fiye da 18, 000 a Jihar Kano Domin Shirya Zaben Shugaban Kasa

Kwamishinoni 4 za su tare a Ribas

Ragowar kwamishonin ‘yan sanda da za su taru suyi aiki a Jihar Kudu maso kudancin kasar su ne Samuel Musa, Lanre B. Sikiru da Aderemi Adeoye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabin da ta fitar, SP Grace Iringe ta ce Kwamishinan da yake Ribas watau CP Okon O. Effiong, zai bar jihar zuwa jihar Enugu domin aikin zaben 2023.

'Yan Sanda
Dakarun 'Yan Sandan Najeriya Hoto : Getty Images
Asali: Getty Images

Rundunar ‘yan sanda tayi kira ga al’umma su fita su zabi ‘yan takaran da suke so a ranar Asabar, suka tabbatar da an shirya yin zaben adalci da gaskiya.

An yi canjin jagorori a Kano

Punch ta fitar da rahoto a ranar Talatar cewa an samu sabon Kwamishinan ‘yan sanda na reshen Kano a yayin da kwanaki kadan suka rage ayi zabe.

Sufetan ‘Yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba ya amince da nadin Muhammad Yakubu a matsayin sabon Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanata Ya Tona Komai, Ya Jero Manyan Gwamnonin PDP da ke Tare da Tinubu a Boye

Daily Trust ta ce CP Muhammad Yakubu zai maye gurbin Kwamishina mai-ci, Mamman Dauda.

Kakakin jami’an, Abdullahi Kiyawa ya ce CP Ita Uku-Udom da DCP Abaniwonda Olufemi za su taimakawa Yakubu a yankin Kudu da Arewacin jihar.

Hakan yana zuwa ne a lokacin da wasu ke zargin CP Mamman Dauda da cafke jagororin adawa musamman ‘yan jam’iyyar NNPP a wasu garuruwa.

Jam’iyyar NNPP ta shiga rububi

Ku na da labari Ibrahim Shekarau ya samu tikitin Sanata a NNPP, amma daga baya ya koma Jam’iyyar PDP, hakan ya na nufin dole ya fasa neman tazarce.

Tuni NNPP ta shirya sabon zaben tsaida gwani, ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga, amma Hukumar INEC ba ta lissafi da shi a cikin masu takaran 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel