Zabe Saura ‘Yan Kwanaki, Jam’iyyar NNPP ta Gano ba ta da ‘Dan Takarar Sanata a Kano

Zabe Saura ‘Yan Kwanaki, Jam’iyyar NNPP ta Gano ba ta da ‘Dan Takarar Sanata a Kano

  • Jam’iyyar NNPP wanda ake yi wa lakabi da mai kwandon kayan marmari ta gamu da cikas
  • Hukumar INEC ba ta san da zaman Rufa’i Hanga a cikin ‘Yan takaran Sanatan Kano ta tsakiya ba
  • Duk da Jam’iyya ta maye gurbin Ibrahim Shekarau da Hanga, INEC ta nuna ita ba ta san an yi ba

Kano - Maganar da ake yi, Rufa’i Hanga bai cikin ‘yan takaran kujerar Sanatoci da hukumar INEC ta fitar da sunayensu a jerin karshe na masu shiga zabe.

A ranar Talata, Premium Times ta kawo rahoto cewa babu sunan Rufa’i Hanga a masu neman kujerar majalisar dattawa a jerin da hukumar INEC ta fitar.

A jiya ne hukumar zabe ta kasar ta saki sunayen karshe na wadanda za su tsayawa jam’iyyunsu, NNPP ba ta ‘dan takaran Sanatan Kano ta tsakiya a 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Makarantan Legit.ng Sun Tsaida ‘Dan Takara Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP

Jam’iyyar adawar mai alamar kayan marmari ta gabatar da sunan Sanata Hanga a matsayin ‘dan takara bayan Ibrahim Shekarau ya sauya sheka zuwa PDP.

Shekarau ya fice daga NNPP

Sanata mai-ci, Ibrahim Shekarau ya yi zama a NNPP na ‘yan kwanaki bayan ya bar APC, daga baya sabani ya jawo ya hakura da jam’iyyar da yin tazarce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce har yanzu sunan Shekarau ake gani a wajen INEC duk da Sanatan ya rubutawa hukumar takarda cewa ya bar NNPP kuma ba zai yi takara ba.

Jam’iyyar NNPP
Yakin neman zaben NNPP a Kano Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Ita hukumar INEC ta na ikirarin Shekarau bai sanar da ita a hukumance cewa ba shi ne ‘dan takaran NNPP ba, don haka a dokar zabe ba za a iya canza shi ba.

Jam’iyyar NNPP ta fake da cewa ra shigar da kara a kotu, kuma Alkali ya umarci INEC ta maye guraben wasu ‘yan takaranta a zaben 2023, amma ba ayi ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Saura kiris zabe, Limaman Katolika sun fadi wadanda za su zaba a zaben bana

Babu sunan Sanata Hanga

Legit.ng Hausa ta bibiyi bayanan da hukumar zabe ta fitar a game da ‘yan takaran da aka canza ko suka gyara sunayensu, a ciki ba a ga Sanata Rufai Hanga ba.

Daga Kano akwai ‘dan takaran Sanatan Arewa, Barau Jibrin wanda aka gyara sunansa.

Haka zalika binciken na mu ya nuna mana a jihar Kaduna akwai Lawal Adamu Usman da Sulaiman Dabo da su ke harin majalisar dattawa da na wakilai.

Peter Obi zai lashe zaben 2023?

Ku na da labari mun tambayi masu karanta labaranmu game da wanda suke so ya zama Shugaban kasar Najeriya a karshen watan Mayun shekarar bana.

Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya tsaya a jam’iyyar adawa ta NNPP, shi ya fara yin zarra da farko, amma ya kare da kusan 28%, yana bayan 'dan takaran LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel