An Dankara ‘Yan Sanda Fiye da 18, 000 a Jihar Kano Domin Shirya Zaben Shugaban Kasa

An Dankara ‘Yan Sanda Fiye da 18, 000 a Jihar Kano Domin Shirya Zaben Shugaban Kasa

  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya yi bayanin matakan inganta tsaro da aka dauka tun wuri
  • CP Mamman Dauda ya ce akwai jami’ai fiye da 18, 000 da aka yi tanadi domin su hana rikicin zabe
  • Dauda ya nuna nasarorin da ‘yan sanda suka samu a wajen cafke masu bangar siyasa a jihar Kano

Kano - Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Mamman Dauda ya ce rundunar jami’an tsaron ta turo dakaru sama da 18, 000 da za su yi aikin zabe.

Daily Trust ta rahoto CP Mamman Dauda yana cewa wadannan jami’an ‘yan sanda za su yi kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a zaben shugaban kasa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa Duniya wannan ne yayin da ya yi wata hira da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda na Kano da ke Bompai.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama matashi bayan yiwa mahaifinsa barazanar kisa a wata jihar Arewa

Baya ga bayanin shiryawa zaben da za ayi a ranar Asabar, Mamman Dauda ya tabbatar da an bada kudi ga iyalan jami’an da suka rasu a bakin aiki.

Irin wannan tukwuici yana cikin alheran da suka saba fitowa daga ofishin Sufeta Janar.

An kama 'yan bangar siyasa

Jaridar ta rahoto CP Dauda ya na bayanin rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Kano sun cafke mutane 365 a cikin makonni bakwai da suka gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan Sanda
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mai girma Kwamishinan ya ce ana tuhumar wadannan mutane da aikata laifuffuka dabam-dabam a lokacin da ake kokarin ayi zabe cikin salin-alin.

Babban jami’in tsaron ya ce a tsawon watanni biyun da suka wuce, ‘yan sanda sun cafke mabiya jam’iyyun siyasa iri-iri kuma a mabanbantan lokuta.

Kamar yadda Kwamishinan ya fada, Ali Sa’idu da wasu mtum 61 sun shiga hannu a lokacin taron yakin neman zaben APC a filin wasan Sani Abacha.

Kara karanta wannan

Magana na Nan: DSS Sun Taso Gwamnan CBN a Gaba, An Cigaba da Binciken Emefiele

Yayin da ‘yan jam’iyyar NNPP suke yawon kamfe a Ja’oji, Dauda ya ce an yi nasarar kama wani Ibrahim Dauda da aka samu dauke da miyagun kwayoyi.

Independent ta tabbatar da cewa an cafke Abdullahi Musa da wasu ‘Yan jam’iyyar APC da kuma mutum biyu da ke goyon bayan NNPP da sunan ta’adi.

‘Yan sanda sun kama mutanen ne da zargin lalata allon ‘yan takara a karamar hukumar Minjibir. Yanzu an gabatar da su a kotu domin ayi shari'a.

An fito da wakilan zabe

Kun samu labari cewa Jam’iyyun siyasa sun bada sunayen mutane fiye da miliyan 1.5 a matsayin wakilan zabensu a rumfunan da ake da su a kasar nan.

Jam’iyyun APC, PDP, NNPP su na da wakilai 145, 000 a Jihar Kano kurum, sannan akwai wakilai fiye da 98, 600 a jihar Legas da wasu 79, 700 a Ribas.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel