Magana na Nan: DSS Sun Taso Gwamnan CBN a Gaba, An Cigaba da Binciken Emefiele

Magana na Nan: DSS Sun Taso Gwamnan CBN a Gaba, An Cigaba da Binciken Emefiele

  • Ma’ikatan hukumar DSS ba su hakura ba, har yau ana bincike a kan Gwamnan bankin CBN a Najeriya
  • Zargin da ke wuyar Godwin Emefiele sun hada da wawurar kudin jama’a da taimakawa ta’addanci
  • Birgediya Janar Tukur Gusau ya yi magana kan yadda sojoji suke gadin Gwamnan babban bankin

Abuja - Jami’an hukumar DSS sun kara kaimi wajen binciken da ake gudanarwa a kan Gwamnan babban banki na CBN watau Mista Godwin Emefiele.

Daily Trust ta ce an cigaba da wadannan bincike ne domin a iya cafke Godwin Emefiele, a gurfanar da shi da zargin yin sata da taimakawa ta’addanci.

A daidai wannan lokaci kuma jami’an sojoji su na ba Gwamnan na CBN kariya dare da rana – a cikin gida da ofis domin ganin sun hana wani ya cafke shi.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Najeriya sun gaji da Buhari, matar Atiku ta yi bayanai masu daukar hankali

Hedikwatar tsaro ta dai musanya zargin cewa sojojin kasa sun zama dogaran Godwin Emefiele.

Bincike ya dawo danye a DSS

Biyo bayan gaza cafke shi da aka yi kwanakin baya, jaridar ta ce jami’an tsaro masu fararen kaya sun dauko sabon bincike, su na yi a kan gwamnan bankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da hukumar ta DSS take so shi ne a gudanar da bincike na musamman a kan tulin zargin da suke kan wuyan Emefiele wanda yake CBN tun 2014.

Emefiele
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Zargin da ake yi wa wannan jami’i sun hada da satar kudi, taimakawa kungiyoyin ta’addanci, kawowa kasa barazanar tsaro da cin dunduniyar gwamnati.

Ma’aikatan DSS sun ki yarda su yi magana da ‘yan jarida a game da wannan lamari, amma rahoton ya tabbatar da cewa ana kan binciken Mista Emefiele.

Wata majiya ta ce jami’an tsaron su na kokarin gamsar da shugaba Muhammadu Buhari ya bada amincewarsa a aikin da ake yi saboda nauyin zargin.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

Godwin Emefiele ya gagara?

Da aka nemi a cafke Gwamnan babban bankin na Najeriya a karshen 2022, sai ya bi tawagar shugaban kasa ya sulale daga Najeriya zuwa kasar Amurka.

Bayan dawowarsa gida, wata majiya ta ce shugaban hafsun tsaro ya bada sojoji da suke gadinsa, lamarin da ko shugaba Buhari bai sani ba sai daga baya.

Rahoton ya ce Darektan yada labaran sojoji, Janar Tukur Gusau ya ce gadin bai saba al’ada ba, yake cewa kare irinsu dole ne saboda kimar da suke da ita.

Buhari bai saba ba - Fashola

A wani rahoto da aka fitar ba dadewa ba, an ji Raji Babatunde Fashola ya ce babu inda Muhammadu Buhari ya sabawa hukuncin kotun koli kan canza kudi.

Wani Ministan kuma ya ce dawo da tsohuwar N200 ba tare da N500 da N1000 ba, raina kotu ne. A wajen Fashola, fahimta fuska ce da kowa da irin ta sa.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel