'Yan Najeriya Sun Gaji da Mulkin Buhari, Cewar Matar Dan Takarar Shugaban Kasa, Titi Atiku Abubakar

'Yan Najeriya Sun Gaji da Mulkin Buhari, Cewar Matar Dan Takarar Shugaban Kasa, Titi Atiku Abubakar

  • Matar dan takarar shugaban kasa a APC, Titi Atiku Abubakar ta ce ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin Manjo
  • Ta kuma bayyana cewa, mata a shirye suke su yi zabe bana, don haka ta shawarci kowa ya fito zabe
  • Saura kiris zabe, har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalolin sabbin kudi a Najeriya don yin kamfen

Yola, jihar Adamawa - Matar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Titi Atiku Abubakar ta jagoranci dubban magoya bayan PDP a titunan Yola don neman kuri’u ga mijinta a zaben bana.

Mata, matasa da sauran gungun masoya ne suka taru a gangamin da aka fara da sha-tale-talen Mai Doki zuwa kofar gidan Atiku a ranar Juma’a 17 ga watan Faburairu.

Da take yiwa jama’a bayani, Titi ta bukaci ‘yan Najeriya da su zabi mijint a matsayin shugaban kasa a zaben da za a yi a makon gobe.

Kara karanta wannan

Karya ne: Fadar Shugaban Kasa ta Karyata Zargin El-Rufai da Ganduje

Matar Atiku ta caccaki Buhari
'Yan Najeriya Sun Gaji da Mulkin Buhari, Cewar Matar Dan Takarar Shugaban Kasa, Titi Atiku Abubakar | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewarta, Atiku ne zai kawo ci gaba Najeriya tare da sharewa ‘yan kasar ciwon talauci da gwamnatin Buhari ta jefa kowa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama’a sun gaji da mulkin Manjo Buhari mai ritaya, inji Titi

Da take sukar gwamnatin Buhari, ta ce APC ta jefa ‘yan Najeriya cikin wahalhalu da tsagwaron talauci babu gaira babu dalili, Daily Trust ta ruwaito.

Ta buga misali da yadda sabuwar dokar kudi ta CBN ta jefa ‘yan cikin wahala, ga kuma yadda karancin man fetur ke kokarin zamewa ‘yan kasar halin ni ‘ya su.

Ta bayyana jin dadinta da yadda ake tallata mijinta da PDP a fadin jihohi 36 na kasar, inda ta bukaci mata da su fito kwai da kwarkwata su yi zabe.

Matar Atiku ta caccaki mulkin Buhari

A cewarta:

Kara karanta wannan

Toh fa: Dan majalisa Doguwa ya ce yana bukatar tsabar N70m na harkallar zabe

“Duk inda miji ya taka, karbarsa ake hannu bibbiyu kuma sakamakon na da kyau, tsammanin na da yawa.
“Mutane sun gaji da wannan gwamnatin. Yunwa ko ta ina, mutane na shan wahala musamman a wannan lamari na kudi da man fetur. Mutane a fusace suke.
“Sama da shekaru bakwai da rabi, mutane sun gaji, suna son sauyin gwamnati. Mata a shirye suke su yi zabe."

Titi ta dura birnin Yola ne a ranar Alhamis da yamma, inda ta samu tarbar dandazon jama’a da magoya baya, ciki har da tawagar matar gwamnan jihar Talatu Fintiri da matar tsohon gwamnan jihar, Zainab Boni Haruna.

A tun farko, Atiku ya ce kada CBN ta kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudi saboda dakile barayin ‘yan siyasa daga samun kudin kamfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel