Adamu, El-Rufai da Wasu Gwamnoni 2 Sun Gana da Malami Kan Canja Naira

Adamu, El-Rufai da Wasu Gwamnoni 2 Sun Gana da Malami Kan Canja Naira

  • Antoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya kai ziyara Sakatariyar APC ta kasa dake Abuja ranar Litinin
  • Malami ya gana da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, da wasu gwamnonin ci gaba uku
  • Ganawar na zuwa ne awanni 24 bayan gwamnoni sama 10 sun tattauna da Adamu kan batun karancin naira

Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gana da Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, yau Litinin 20 ga watan Fabrairu, 2023.

Vanguard ta ce gwamnonin APC uku da suka kai ƙarar FG gaban Kotun koli sun halarci ganawar wacce ta gudana a babban Sakatariyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu.
Adamu, El-Rufai da Wasu Gwamnoni 2 Sun Gana da Malami Kan Canja Naira Hoto: APC
Asali: UGC

Gwamnonin da suka halarci taron su ne, Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na Kogi da kuma Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Hargitse, Jam'iyya Ta Ayyana Gogon Baya ga Peter Obi a Zaben 2023

Bayan waɗan nan gwamnonin, rahoton Daily Trust ya ce shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba (PGF) kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya halarci zaman a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taron wanda ya shafe kusan awa ɗaya na zuwa ne awanni 48 gabanin ci gaba da sauraron shari'a kan sauya fasalin naira da CBN ya tsiro da shi a gaban Kotun koli ranar Laraba mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku cewa Kotun koli ta umarci babban bankin Najeriya da ya dakatar da yunkurinsa na kakaba 10 ga watan Fabrairu, 2023 a matsayin wa'adin dena amfani da tsoffin N200, N500 da N1000.

Amma CBN ya yi fatali da hukuncin Kotun inda ya jaddada cewa tsoffin takardun naira sun tashi aiki tun ranar Jumu'a 10 ga watan.

Bayan zaman ranar 15 ga watan Fabrairu, Kotun fa sake ɗage ƙarar zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Abun Ya Wuce Tunani: Jerin Sunayen Gwamnonin APC 14 da Suka Shirya Yaƙar Tsarin Sauya Naira Na CBN

Kana Shirin Gayyato Mana Rashin Bin Doka, Wike Ya Sake Tura Sako Ga Buhari

A wani labarin kuma Wike ya gargaɗi Buhari kan abinda ka iya faruwa bayan ya take umarnin Kotun koli game da tsoffin naira

Gwamnan jihar Ribas ya nuna rashin jin daɗinsa game da matakin shugaban kasa ya ɗauka na haramta amfani da N500 da N1000 tun daga ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Tsarin sauya naira da CBN ya bullo da shi ya haddasa kace-nace duba da yananin da yan Najeriya suka tsinci kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel