Kana Shirin Gayyato Mana Rashin Bin Doka, Wike Ya Sake Tura Sako Ga Buhari

Kana Shirin Gayyato Mana Rashin Bin Doka, Wike Ya Sake Tura Sako Ga Buhari

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya shawarci shugaba Buhari ya canja tunani, ya bi umarnin Kotun kolin kan tsoffin naira
  • Wike ya ce ƙin bin umarnin Kotu da shugaban kasa ya yi, yana gayyatoo rashin bin doka da kama karya ga ƙasa
  • Jagoran G-5 a PDP ya ce mutanen Ribas ba zasu sabi duk ɗan takarar da ya nuna jin daɗi da wahalhalun yan Najeriya ba

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya girmama umarnin Kotun koli kan tsaffin takardun naira.

Gwamna Wike ya yi wannan magana ne a wurin ralin kamfen PDP ta jihar Ribas wanda ya gudana a garin Ngo, ƙaramar hukumar Andoni, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Wike.
Kana Shirin Gayyato Mana Rashin Bin Doka, Wike Ya Sake Tura Sako Ga Buhari Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

A ranar Alhamis, shugaba Buhari ya umarci babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita wa'adin halascin amfani da tsohuwar N200 zuwa 10 ga watan Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Yi Halinta: An Gano Mutum 2 Da Suka Sauya Wa Buhari Tunani Kan Tawaita Wa'adin N500 da N100

Buhari ya ce 'yan Najeriya na da cikakkiyar dama duk da wa'adi ya cika su maida tsoffin takardun N500 da N1000 zuwa CBN da sauran wuraren da aka ware tsawon

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ƙasan ya ba da wannan umarni ne duk da hukuncin Kotun ƙoli wanda ya nuna tsoffin naira na nan da martabarsu ta halastattun kuɗi har zuwa lokacin da zata yanke hukuncin ƙarshe.

Bana goyon bayan tsarin sauya naira - Wike

Da yake tsokaci kan ci gaban, gwamna Wike ya ce ba ya tare da tsarin sauya fasalin kuɗi saboda ya kawo ƙarin wahala da ƙunci ga 'yan Najeriya.

A ruwayar Leadership, Ya ce:

"Na yi amanna da ƙasa mai bin doka sau da ƙafa, ya kamata shugaban kasa ya girmama hukuncin Kotun koli, matukar ba zaka bi umarnin Kotun koli ba to kana shirin jawo mana tashin hankali."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna

"Saboda haka mu a jihar Ribas, mun yi Allah wadai da matakin shugaban kasa na ƙin bin umarnin Kotun ƙoli. Muna bayan Mulkin Dimukuradiyya kuma ba zai tabbata ba sai da bin doka."

Ba zamu zabi ɗan takarar dake goyon bayan tsarin CBN ba - Wike

"Don haka duk wani ɗan takarar da yake goyon bayan wannan tsarin wanda ya jefa mutane cikin wahala, ba zamu taɓa goyon bayansa ba."
"Duk wani tsari da kake son aiwatarwa ya kamata ka ba da isasshen lokaci saboda ka kai matsayin da kake ne da kuri'un mutane. Idan tsarin zai kuntatawa al'umma ya dace ka sake tunani."

- Nyesom Wike.

A wani labarin kuma mun kawo maku Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000

Ga dukkan alamu zargin gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, ya yi na wasu mutane a Aso Rock akwai ƙamshin gaskiya domin gaskiya ta fara halinta.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

An gano wasu mutum 2, Minista da Hadimin Shugaban ƙasa, da suka canja tunanin Buhari kan tsoffin N500, N1000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel