Ku Zabi Tinubu, Shine Zabi Na, Kuma Dan Najeriya Ne Na Gari, Inji Buhari

Ku Zabi Tinubu, Shine Zabi Na, Kuma Dan Najeriya Ne Na Gari, Inji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kwarin gwiwarsa game da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu
  • Shugaba Buhari ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su zabi Tinubu a zaben mako mai zuwa da za a yi na shugaban kasa
  • A cewar Buhari, Tinubu ne zai iya daurawa daga inda ya tsaya a mulkinsa, don haka ya amince da nagartarsa ya gaje shi

Najeriya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kadan daga halayen Tinubu, kana ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su zabe shi a zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba.

Shugaba Buhari ya bayyana kwarin gwiwarsa ne ga Tinubu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa, ya yarda nagartar dan takarar shugaban kasan na APC.

Kara karanta wannan

Nasan kuncin da kuke ciki: Buhari ya ji tausayin talakawa, ya fadi magana mai taba zuciya

Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu ne dan takarar shugaban kasa da jam'yyar APC ta fitar a zabenta na fidda gwani da ya gudana a shekarar da ta gabata.

Buhari ya ce ya yarda da Tinubu
Ku Zabi Tinubu, Shine Zabi Na, Kuma Dan Najeriya Ne Na Gari, Inji Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan kira na Buhari kuma na zuwa ne kwanaki shida cif kadin yin zaben shugaban kasa da Najeriya ta sanya a gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bana takara, amma na yarda da Tinubu, cewar Buhari

Da yake bayyana matsayarsa ga zaben bana, Buhari ya ce shi ba dan takara bane a bana, amma zai tabbatarwa 'yan Najeriya wanda ya kamata su zaba.

A cewarsa, ya hango alherai da yiwuwar daurawa daga inda ya tsaya a tattare da Boka Tinubu.

A cewarsa:

"Ni ban dan takara bane a zabe mai zuwa, amma jam'iyya ta, APC, na da dan takara mai suna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ina kira gare ku duk ku zabei Tinubu. Abin yarda ne, cikakken mai imani da Najeriya, kuma zai gina daga abubuwan da muka cimma."

Kara karanta wannan

Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP

Karancin kudi zai iya shafar zabe, inji hukumar zabe ta INEC

A wani labarin kuma, kun ji yadda shugaban hukumar INEC ya bayyana tsoron cewa, watakila karancin sabbin Naira ya shafi zaben bana.

Ya bayyana hakan ne yayin wani zaman masu ruwa da tsaki a zaben bana da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Idan baku manta ba, Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudin da aka buga a kwanakin baya daga CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel