Naira: Shugaba Buhari Na Yiwa Kotun Koli Karan-Tsaye, Bai Dace Ba: Kakakin Majalisa

Naira: Shugaba Buhari Na Yiwa Kotun Koli Karan-Tsaye, Bai Dace Ba: Kakakin Majalisa

  • Kaakin majalisa ya caccaki shugaban kasa bisa abinda ya kira sabawa umurnin kotun koli da gayya
  • Shugaba Buhari ya yi jawabi wa yan Najeriya da safiyar Alhamis misalin karfe bakwai na safe
  • Daga bisani ya shilla kasar Ethiopia domin halartar taron gangamin shugabannin kasashen Afrika

Abuja - Kakakin majalisar wakilai ya yi tsokaci kan jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari yayi ranar Alhamis inda ya baiwa bankin CBN wasu umurni kan sabbin Naira.

Gbajabiamila yace umurnin da Buhari ya bada na dawo da tsaffin N200 na da kyau amma wannan karan-tsaye ne ga hukuncin kotun koli.

A jawabin da ya fitar ranar Alhamis, Gbajabiamila ya ce ba zai kyautatu a ce mutum irin shugaban kasa ne zai rika fito-na-fito da hukuncin kotu ba.

A cewarsa, ya kamata ace Buhari ya saurarawa hukuncin karshe na kotun koli kafin ya furta wani abu.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

Gbajabiamila
Naira: Shugaba Buhari Na Yiwa Kotun Koli Karan-Tsaye, Bai Dace Ba: Kakakin Majalisa HOto: HouseNGR
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya yi kira ga yan Najeriya su yi hakuri da wannan hali da suke ciki.

Yace:

"A yau yan Najeriya, har da baki, na shan bakar wahala da babu gaira babu dalili. Suna kwashe awanni a layin bankuna kawai don su cire kudadensu na cin abinci."
"Bamu san manufarsu ba kan dagewa kan aiwatar da wannan tsari da ka iya tada hayaniya a kasar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel