Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai

Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai

  • Nasir El-Rufai ya ce jami’an gwamnatin tarayya na neman su domin ayi sulhu kan karar da suka kai
  • Gwamnoni su na shari’a da gwamnatin kasar a kotun koli a dalilin sauya manyan takardun kudi
  • El-Rufai ya nuna ba su karbi tayin da aka gabatar masu ba, za su nemi kotun koli ta yanke hukunci

Abuja - A ranar Laraba, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa jami’an gwamnatin tarayya su na rokon su yi sulhu da gwamnonin da suka shigar da kara a kotu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fitar da jawabin musanya rade-radin cewa gwamnoni sun yi zama da gwamnatin tarayya a kan batun canjin kudi.

A rahoton da aka samu, Muyiwa Adekeye wanda ya fitar da jawabi a madadin Gwamnan Kaduna ya ce takwarorinsa ba su yi zama da shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: El-Rufai ya tona asirin Buhari da CBN kan batun tsawaita wa'adin tsoffin Naira

Jawabin ya ce gwamnatin tarayya tana so ne a ba ada damar cigaba da amfani da N200 kadai a matsayin takardar kudi daga yanzu har zuwa 10 ga Afrilu.

CBN sun lalata tsofaffin kudi?

A cewar Gwamnan, gwamnatin tarayya na ikirarin CBN ya lalata tsofaffin N500 da N1000 da aka karba, amma wadanda suke da na su, za sui ya kai masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan talabijin na Channels ta rahoto Malam El-Rufai ya na cewa amfani da N200 kadai ba zai isa ba idan aka yi la’akari da irin wahalar da jama’a suke sha.

Buhari
Buhari a taron FEC Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Tun farko Gwamnan bai yarda cewa bankin CBN ya kona ragowar kudin ba, kuma ya ce za a bukaci akalla shekara daya kafin a iya buga Naira tiriliyan 1.

Alkaluman da ake fitarwa ba daidai ba ne, El-Rufai ya kara da cewa masu neman a sasanta da yawun gwamnati su na fitar da bayanan da ba gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

Babu maganar yin sulhu - El-Rufai

Yayin da gwamnatin tarayya ta bukaci a sasanta ba tare da an je kotu ba, Gwamna El-Rufai ya nuna kai-tsaye suka yi watsi da bukatun da aka gabatar.

A rahoton Daily Trust, an fahimci Gwamnan ya zargi gwamnatin kasar da rashin gaskiya, ya ce su na sa ran kotun koli tayi masu adalci a wannan shari’a.

A karshe, El-Rufai ya ce zai yi wa mutanen jihar Kaduna cikakken bayanin halin da aka shiga da kuma tasirin tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin kudi.

Kaduna vs Gwamnatin kasa

A wani labari na dabam, kun ji cewa wani babban Lauya, Abdulhakeem Mustapha ya tsayawa Gwamnatin Kaduna, ya kai karar gwamnatin tarayya a kotu.

Gwamnatin Buhari ta dauko hayar Ministan shari’a a Gwamnatin Obasanjo domin ya kare ta. Kanu Agabi (SAN) ya musanya zargin Barista Mustapha (SAN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel