El-Rufai Ya Ajiye Kara, Ya Sake Maka Gwamnatin Buhari a Kotu Saboda Canza Kudi

El-Rufai Ya Ajiye Kara, Ya Sake Maka Gwamnatin Buhari a Kotu Saboda Canza Kudi

  • Gwamnatin jihar Kaduna za tayi wata shari’a da gwamnatin tarayya a kan batun canza Nairori
  • Wannan karo, Abdulhakeem Mustapha ne ya shigar da kara a madadin Gwamnatin Kaduna
  • Jihar Arewacin Najeriyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin yi wa hukuncin kotun koli biyayya

Abuja - A wani karo na dabam, an fahimci Gwamnatin jihar Kaduna tayi karar gwamnatin tarayya da kuma babban banki na kasa watau CBN a kotu.

Jaridar Aminiya ta ce an shigar da wannan kara a gaban Alkali ne saboda gwamnatin tarayya ta kin yin biyayya ga umarnin kotu a kan karin wa’adi.

Kotun koli ta yanke hukunci cewa a cigaba da amfani da tsofaffin takardu a matsayin kudi kafin a zartar da hukunci a kan karar da wasu jihohi suka kai.

Rahoton ya ce lauyan gwamnati, Abdulhakeem Mustapha (SAN) ya shigar da karar da sunan jihar Kaduna, maganar ta je kotu ne a ranar Litinin dinnan.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Ba ayi wa kotu biyayya ba - Kaduna

A zaman da aka yi a karkashin jagorancin Alkali Inyang Okoro, Barista Mustapha SAN ya ankarar da kotu kan rashin biyayyar gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan shari’an Najeriya, Kanu Agabi (SAN) wanda ya tsayawa gwamnatin tarayya a kotun, ya musanya duka zargin wannan babban lauya.

El-Rufai
Nasir El-Rufai da Yahaya Bello Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Kanu Agabi ya yi kokarin gamsar da Okoro cewa gwamnati ba ta bijirewa umarnin kotu ba.

A gefe guda, kotun ta bada umarni cewa a tanadin bayanan da ake bukata wajen shigar da kara nan da gobe da na gabatar da martani a makon gobe.

A ranar Laraba ake sa ran za a cigaba da sauraron wannan kara domin jin ko gwamnati ta ki yin biyayya ga hukuncin Alkalan kotun kolin kasar.

Ana bugawa a kotun koli

Baya ga wannan kara da ke gaban kotun tarayya da ke Abuja, ana shari’a tsakanin Gwamnonin jihohi da-dama da gwamnatin tarayya a gaban kotun koli.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai

A kotun koli, Lauyan da ya tsayawa gwamnatin Kano, Sunusi Musa SAN ya nemi alfarma a canza lokacin sauraron shari’arsu da gwamnatin tarayya.

Sanusi II a Kano

A makon yau aka ji labari cewa magoya baya kamar su lashe Mai martaba, Sarki Muhammadu Sanusi II da aka tunbuke a 2020 ya shigo mahaifarsa.

Muhammadu Sanusi II ya nufi zuwa ta'aziyya a Dutse, amma ya ce jirginsa ba zai iya zuwa Jigawa kai-tsaye ba, don haka dolensa sai ya biyo ta jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel