El-Rufai da Gwamnonin da Suka Maka Buhari a Kotu Sun Ki Amincewa da Kara Wa’adi Zuwa 10 Ga Afrilu

El-Rufai da Gwamnonin da Suka Maka Buhari a Kotu Sun Ki Amincewa da Kara Wa’adi Zuwa 10 Ga Afrilu

  • Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ta zo da sabon salon yaudara kan tsoffin Naira
  • Gwamnan ya ce, ba a gana da gwamnoni ba kan batun kara wa'adin amfani da tsoffin Naira a Najeriya ba
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana kan yadda a kasar nan wasu ke zanga-zangar nuna adawa da shirin gwamnati

Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana dalla-dalla lamarin da ke tattare da kudurin gwamnatin Buhari na tsawaita wa’adin kashe tsoffin kudi a Najeriya.

TheCable a baya ta ruwaito cewa, gwamnatin Buhari na duba yiwuwar tsawaita wa’adin amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 zuwa 10 ga watan Afrilu.

Sai dai, gwamnan Kaduna a cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun mai ba shi shawari kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya ce, gwamnonin da suka maka Buhari a kotu sun nesanta kansu da batun karin.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Bayan Zaman Kotun Koli, Shugaba Buhari Ya Sake Kus-Kus da Emefiele, Bayanai Sun Fito

Halin da ake ciki game da sabbin Naira
El-Rufai da Gwamnonin da Suka Maka Buhari a Kotu Sun Ki Amincewa da Kara Wa’adi Zuwa 10 Ga Afrilu | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

A banagare guda, Malam Nasiru El-Rufai ya shaida cewa, akwai alamu masu nuna kura-kurai daga majiyar jaridar TheCable, inda yace gwamnoni basu gana da Buhari ba a cikin wannan makon.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda ta kaya kan batun tsoffin kudi

Sai dai, ya ce akwai manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya sun kira wasu gwamnoni game da batun da ya shafi sabbin Naira da kuma karar da gwamnonin suka shigar.

Ya amsa cewa, tabbas gwamnatin tarayya ta gabatarwa wasu daga cikin gwamnonin ta waya cewa, za a tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin N200 zuwa 10 ga watan Faburairu.

A gefe guda, ya ce an shaidawa gwamnonin cewa, CBN tuni ya lalata tsoffin N500 da N1000 da aka mayar banki, don haka ba zai yiwu a same su ba.

Sai dai, da yake karin bayani, El-Rufai ya ce:

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

“Sun san da haka, shi yasa suka yi ikrarin karya cewa CBN ya lalata tsoffin N500 da N1000. Wannan ya saba da gaskiyar abin da gwamnoni suka sani na cewa tsoffin kudin suna nan a bankunan kasuwanci har sai ranar 13 ga watan Faburairu, karya ne babu N500 da N1000 tsoffi da aka lalata.”

A yau Laraba 15 ga watan Faburairu kotun ta sake dage zaman karar da gwamnonin suka shigar zuwa ranar 22 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel