Sarkin Ibo Ya Yi wa Shugaban Kasa Abin da ba Zai Manta ba Har ya Bar Duniya

Sarkin Ibo Ya Yi wa Shugaban Kasa Abin da ba Zai Manta ba Har ya Bar Duniya

  • Muhammadu Buhari ya samu sarauta a wajen yi wa Bola Tinubu kamfe a Kudancin Najeriya
  • Shugaban kasar ya zama "Nwanne D'namba'' a kasar Ibo, saboda irin kaunar da ya nunawa yankin
  • Buhari ya ce ba zai taba mantawa da karramawar Sarki Emmanuel Chukwuagina Okeke CFR ba

Imo – Shugaban Muhammadu Buhari ya samu sarautar gargajiya daga majalisar Sarakunan jihar Imo a ranar Talata, 14 ga watan Fubrairu 2023.

Kamar yadda Buhari Sallau ya bayyana a shafinsa na Facebook, Mai girma Muhammadu Buhari ya samu sarautar "Nwanne D'namba'' a Owerri.

Wannan sarauta ta na nufin shugaban Najeriyan ‘danuwan kasar Ibo ne da yake ketare, ganin irin kaunar da ya nunawa yankin Kudu maso gabas.

Mai martaba Eze Dr. Emmanuel Chukwuagina Okeke CFR ya yabi shugaban kasar da cewa yana kaunar jama’arsa, kuma ya kawo masu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Dalilin Canza Kudi, Mai Martaba Ya Koka da CBN, Babu N20, 000 a Cikin Fadar Sarki

Buhari ya yi wa Sarki godiya

Da yake jawabi, rahoton ya ce Muhammadu Buhari ya godewa Sarki Emmanuel Chukwuagina Okeke a kan wannan karramawa ta musamman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nagode da wannan girma da ba zan taba mantawa ba har karshen rayuwata. Mun gode da aka tara manya domin su tarbe mu.
Mun fuskanci kalubale, an shiga mawuyacin hali a kasar nan kuma mu ka ga cewa abin da ya fi shi ne kasar ta zauna a tare.

- Muhammadu Buhari

Sarkin Ibo
Jagororin APC a Owerri Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A jawabin da ya gabatar, Buhari ya yi kira ga mutanen kasar nan da su kaunaci junansu, su zama masu zumunci tare da kokarin ganin an zauna lafiya.

Buhari ya ce Ubangiji ne ya daura su a mulki ta silar jam’iyyarsu ta APC mai rike da shugabanci.

The Eagle ta rahoto Buhari yana cewa ya zo jihar Kudu maso gabashin kasar ne domin tallata Bola Tinubu wanda yake so ya zama magajinsa a Aso Rock.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya

Bayan ya zagaya da ‘dan takaran zuwa Nasarawa, Katsina, Bauchi da Sokoto, shugaban kasar ya ce a shirye yake ya cigaba da tallata takarar Tinubu.

Kiran Sarkin Iwo a kan canjin kudi

An ji labari Mai martaba Sarkin Iwo, Abdurosheed Akanbi ya na fatan Gwamnatin tarayya za tayi amfani da ranar masoya domin jin kan al’ummarta.

Sarkin yake cewa ‘Yan Najeriya su na shan wahala sosai, ya ce a matsayinsa na Basarake, ba zai iya bugun kirji cewa ya na da N20, 000 a fadarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel