Dole Gwamnati Mai Zuwa Tayi Koyi da Shugaba Muhammadu Buhari, Inji Boss Mustapha

Dole Gwamnati Mai Zuwa Tayi Koyi da Shugaba Muhammadu Buhari, Inji Boss Mustapha

  • Sakataren gidan gwamnati a Najeriya ya bayyana cewa, akwai abubuwan koyi a gwamnatin Buhari
  • Boss Mustapha ya bayyana cewa, ya kamata shugaba na gaba ya duba ga abubuwa da na mulkin Buhari
  • Saura kwanaki kadan a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, hakan ne zai kawo karshen mulkin shugaba Buhari

FCT, Abuja - Sakataren gidan gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana shawarin cewa, akwai babban abin koyi a gwamnatin Buhari da ya kamata duk wata gwamnati mai zuwa ta koya, rahoton Punch.

Boss ya bayyana cewa, gwamnatin Buhari ta koyi wasu manyan darussa da ya kamata su zama izina ga gwamnatin da za ta gaje ta.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta taka rawar gwani wajen kawo ci gaba a fannin taimakawa hukumomin gwamnati ta fuskar shugabanci na gari da kuma gyara a tsarin dimokradiyya.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya

Buhari abin koyi ne ga shugaba na gaba
Dole Gwamnati Mai Zuwa Tayi Koyi da Shugaba Muhammadu Buhari, Inji Boss Mustapha | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da majalisar mika mika mulki da shugaban kasa Muhammadu ya rantsar a ranar Talata 14 ga Faburairu, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aikin majalisar mika mulki ta Buhari

Majalisar dai babban aikinta shine tabbatar da mika mulki bayan zabe daga Buhari zuwa shugaba na gaba zai zo bayan zaben watan Faburairu, TheCable ta ruwaito.

Har ila yau, majalisar za ta tabbatar da mika mulki cikin tsanaki, tsara tsaron shugaban kasa da mataimakinsa na gaba da kuma tabbatar da kasa ta zauna lafiya bayan zaben bana.

Idan baku manta ba, kwanaki kadan ya rage a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, kuma hakan na nuni da shugaba Buhari ya shafe shekaru takwas yana jan ragamar kasar nan.

Buhari na ci gaba da bayyana cewa, ya cika dukkan alkawuran da ya dauka, sai dai wasu 'yan Najeriya na ganin shugaban ya gaza ta wasu hanyoyin.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga

Ba Ma Tunanin Yiwuwar Dage Zaben Bana, in Ji Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC

Yayin da aka yada jita-jita cewa, za a dage zaben bana saboda matsalolin karancin sabbin Naira, hukumar zaben ta fito ta yi magana mai daukar hankali.

An fitar da sanarwar da ke cewa, hukumar a shirye take domin yin duk mai yiwuwa don tabbatar da an yi zabe bana.

Ta kuma yi watsi da dukkan labaran karya da ake yadawa game da soke zaben 2023 mai zuwa nan ksua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel