Ba Ma Tunanin Yiwuwar Dage Zaben Bana, in Ji Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC

Ba Ma Tunanin Yiwuwar Dage Zaben Bana, in Ji Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, tabbas za a yi zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba
  • An yada wasu rahotannin karya da ke cewa, za a dage zaben bana saboda karancin Naira da ake fuskanta
  • Shugaban INEC ya gana da gwamnan CBN, ya ba shi tabbacin za a samu kudi don yin aikin zaben bana

FCT, Abuja - Hukumar zabe ta INEC ta nesanta kanta da wata sanarwa da ke yawo mai cewa, za a daga zaben 2023 mai zuwa.

An yada wata jita-jita a ranar Litinin 13 Faburairu, 2023 cewa, hukumar zabe na duba yiwuwar dage zaben 2023 zuwa ranar 4 ga watan Maris na bana saboda karancin Naira da ake fuskanta.

Wani rahoton ya kuma ambato shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu na cewa, karancin kudin da ake fama dashi a kasar ya shafi hukumar kuma dage zaben ne mafi kyau ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba Gwamnan Arewan da Zai Iya Kawowa Tinubu Kuri'un Jiharsa, Tsohon Shugaban NHIS

Ba za a dage zaben bana ba, inji INEC
Ba Ma Tunanin Yiwuwar Dage Zaben Bana, in Ji Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC | Hoto:Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Ba gaskiya bane, INEC ta bayyana gaskiyar batu

Da yake martani ga rahotannin, mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi ya shaidawa TheCable cewa, dukkan rahotannin karya ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta tattaro daga jawabansa cewa:

“Ba gaskiya bane. INEC ba za ta yi ba, kuma ba ta tunanin dage babban zaben 2023.
“Don kawar da shakku, za a yi zaben shugaban kasa/na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Faburairu, yayin da za a yi zaben gwamnoni/na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris."

A tun farko kun ji cewa, shugaban INEC ya gana da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wanda ya tabbatar masa za a samar da wadatattun kudade don yin zaben 2023.

Ba za a yi zabe a wasu rumfuna 240 ba a Najeriya

Kara karanta wannan

INEC Na Goyon Bayan Wani Ɗan Takara Ko Jam'iyya a 2023? Mahmud Yakubu Ya Tsage Gaskiya

Sai dai, a wani rahoton da INEC ta fitar, ta ce ba za a yi zabe a wasu yankuna daban-daban na Najeriya a bana.

Hukumar ta kafa hujja da cewa, a rumfunar 240, babu wadanda suka yanki katin yin zabe, don haka ba zai yiwu a kai kayan zabe inda babu mai yin zabe ba.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da zura ido ga hukumar zabe don ganin gudun ruwanta a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel