Tinubu Zai Share Hawayen Yan Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Buhari

Tinubu Zai Share Hawayen Yan Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Buhari

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce idan Bola Tinubu ya gaje shi zai iya kawar da matsalolin Najeriya
  • A wurin ralin jihar Imo ranar Talata, Buhari ya gode wa dubun-dubatar mutanen da suka halarci filin wasan Dan Anyiam
  • Kafin zuwa wurin kamfen, shugaban ya kaddamar da Tituna guda biyu da gwamnatin Imo ta kammala

Imo - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyarsa APC, Bola Tinubu, zai share hawayen Najeriya idan ya zama magajinsa.

Vanguard ta ce Buhari ya ba da wannan tabbacin ne yayin da yake jawabi ga dandazon magoya baya da suka halarcin ralin kamfen APC a filin kwallon Dan Anyiam dake Imo ranar Talata.

Ralin APC a Imo.
Tinubu Zai Share Hawayen Yan Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce:

"Na zo nan ne domin Asiwaju, muna godiya gare ku, babu abinda zamu ce muku sai dai mu ƙara gode maku, mun gode."

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi da Zamu Saka Wa Tinubu Alherin Da Ya Mana, Gamayyar Yan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yau gamu a gabanku, mun yaba sosai da yanayin yadda kuka bamu lokacinku kuka hito, mun ji dadi sannan nun yaba da irin goyon bayan da kuka nuna mana."
"Ina tabbatar maku da cewa Asiwaju zai share muku hawaye idan ya zama shugaban ƙasan Najeriya na gaba, muna kara godiya a gareku."

Shugaba Buhari, Bola Tinubu, gwamnonin APC da sauran jiga-jigai da ƙusoshin jam'iyya sun halarci ralin ɗan takarar shugaban ƙasa a Anyiam stadium, jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Buhari ya kaddamar da titin MCC mai tsawon kilomita 15km da Titin Urratta kana daga bisani ya kama hanyar zuwa wurin da aka shirya ralin.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa shugaban ƙasa ya isa wurin da misalin ƙarfe 1:25 na rana tare da rakiyar gwamnan Imo, Hope Uzodinma.

Daga isarsa, kai tsaye ya zarce zuwa kan dandamalin da aka tsara wanda Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima zasu tsaya su yi jawabi ga magoya baya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Wakilta Pantami, Ya Faɗi Wanda Shugaban Kasa Ke Goyon Baya 100 Bisa 100 a Zaben 2023

Bamu Goyon Bayan Kowane Dan Takara - Amurka

A wani labarin kuma Gwamnatin Amurka ta bayyana matsayarta game da goyon bayan wani ɗan takara a zaben Nakeriya 2023

Mataimakiyar sakataren hukumar kula da harkokin kasashen Afirka ta Amurka, Molly Phee, ta ce Amurka ba ta da wani wanda take goyon baya a zaɓen 2023.

Yayin da ta jagoranci tawaga suka kai ziyara Hedkwatar INEC, Phee ta ce sun maida hankali ne wajen ganin an gudanar da zaɓe mai inganci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel