Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Yawo

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Yawo

  • Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya ya tattauna da takwararsa na Dubai
  • Kimanin shekara guda kenan da aka hana yan Najeriya shiga hadaddiyar daular larabawa saboda dalilai
  • Buhari ya roki Sarkin kasar ya sassautawa Najeriya bisa wannan doka saboda a cigaba da alaka

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki takwararsa na Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan na a sassauta takunkumin da aka kakabawa yan Najeriya na hanasu shiga Dubai.

Yan Najeriya da dama na shiga birnin ta Dubai domin kasuwanci da yawon ganin Ido.

Shugaban yayi haka ne ta wani hira da sukayi ta hanyar tangaraho da shugaban kasar Dubai din, rahoton DailyTrust.

Tunda fari dai, Buhari ya kira Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne domin yayi masa jaje abisa mutuwar surukar sa, malama Maryam Al-Falasi, a yayin gudanar da wata tattaunawa mai muhimmanci tsakanin kasashen guda biyu.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

BUhari
Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Yawo Hoto: UAE
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, ya shaida cewa Shugaba Buhari ya bukaci takawaran nasa na daya kara duba hana bawa yan najeriya masu burin shiga kasar sa da yayi.

Ya tabbatar da cewa, sa-toka-sa-katsin da yake faruwa tsakanin ofisoshin kasashen nan guda biyu sakamakon halayyar daidaikun yan Najeriya marasa kishin kasa, an riga da tuni an warware su a jakadance, tare da kara tabbatar da cewa babu wata kasa da zata yadda da ayyukan bata gari ko wace iri ce.

To amma, shugaba buhari ya kara jaddada cewar, gwamnatin Najeriya da yake jagoranta a shirye take ta hukunta duk wani mai aikata laifuka a kasar Dubai ta hanyar bin matakan doka da aka tsara a shari’ance.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa

Sannan, shugaban ya kara da tabbatar da cewa, a kyale hukumomin da abin ya shafa dasu wararware shi a tsakanin kasashen guda biyu masu albarka.

Bayanin ya kara da cewa, tuni ma shugaba Buhari ya bada umarnin da kamfanin jigilar jiragen sama na Emirates da yaci gaba da hada hada a lunguna da sakuna na kasar nan.

Idan dai za'a iya tunawa, tun wajen 2022 ne dai kamfanin jigilar jiragen sama na Emirate ya tsaida ayyukan sa a ilahirin kasar nan sakamakon gaza biyan kudade da gwamnatin najeriya take binsa.

Sai dai kuma shugaba Buhari ya tabbatarwa Shugaban Dubai cewa lamarin na kamfanin Emirate yana samun kulawa ta musamman daga gwamnatin najeriya, hada da sauran kamfanunnuka mallakin kasashen waje, domin tuni aka umarci babban bankin najeriya na CBN daya kara basu adadin kudaden kasar waje domin gudanar da ayyukan sub a tare da samun wani balahira ba ga kamfanin.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Asali: Legit.ng

Online view pixel